ADC Ta Cimma Matsaya da Atiku, Peter Obi da Amaechi kan Batun Takara a Zaben 2027

ADC Ta Cimma Matsaya da Atiku, Peter Obi da Amaechi kan Batun Takara a Zaben 2027

  • Yayin da ake fargabar yiwuwar tarwatsewar Atiku Abubakar, Peter Obi da Rotimi Amaechi, jam'iyyar ADC ta ce babu abin da zai raba jagororin hadaka
  • Mataimakiyar kakakin ADC ta kasa, Jackie Wayas ta ce shugabannin sun amince za su marawa duk wanda ya samu tikitin takara baya a 2027
  • A cewarta, jam'iyyar ADC da duka shugabanninta sun kudiri aniyar ceto Najeriya daga kakanikayin da take ciki a yanzu duk da bambancin burinsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam’iyyar hadaka, ADC, ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa manyan shugabanni adawa, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi da Rotimi Amaechi, za su hada kansu don kawo sauyi a kasar nan.

Jam'iyyar ADC ta ce manyan kusoshin adawar sun shirya dunkulewa wuri daya su goyi bayan duk wanda daga cikinsu ya samu tikitin takarar shugaban kasa a 2027.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa APC ta lashe mafi yawan zabukan cike gurbi da aka yi a Kano da jihohi 12'

Atiku da manyan kusoshin ADC.
Hoton Atiku, Amaechi, El-Rufai da manyan jagororin hadaka a taron da suka gudanar a Abuja Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin Jackie Wayas, Mataimakiyar Sakatariyar Yaɗa Labarai ta ADC, a wata hira da jaridar Vanguard ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC za ta bai wa Kudu takarar 2027?

Jackie Wayas ta bayyana cewa ADC na ci gaba da tattaunawa kan ko za ta ba wani yanki tikitin takarar shugaban kasa ko kuma za ta bar kofa a bude ga kowane dan kasa.

Ta ce za a yanke hukuncin ƙarshe ne bayan tattaunawa a cikin jam’iyya da kuma ƙa’idojin da kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) zai tsara kafin babban taron jam'iyya.

“Akwai matsin lamba sosai kan batun karba-karba amma har yanzu ba mu yanke shawara kan yankin da za a ba tikitin shugaban ƙasa ko mu bar shi a buɗe ba.
"Dole mutum ɗaya ne kawai zai samu tikiti takarar ADC a 2027, don haka yanke shawara a kan tsarin karba-karba ko barinsa a buɗe ya dogara ne da tattaunawar cikin gida da kuma ƙa’idojin NEC."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta biya wa Kiristoci rabin kudin kujerar ziyara zuwa Isra'ila

- In ji Jackie Wayas.

A cewarta, babban burin ADC shi ne ceto Najeriya daga matsalolin da take ciki yanzu da kuma sanya maslahar ƙasa sama da komai, rahoton Premium Times.

Wace matsaya Atiku, Obi da Amaechi suka cimma?

Ta ce yarjejeniyar da ta haɗa Atiku, Obi da Amaechi ta wuce burin kowane ɗaya daga cikinsu, domin an gina ta ne a kan ƙuduri ɗaya na gina Najeriya.

“Burin ceto da sauya Najeriya ita ce ta haɗa waɗannan shugabannin adawa da kuka ambata, kuma ita za ta ci gaba da haɗa su,” in ji ta.
Tambuwar da Obi a taron ADC.
Hotun Tambuwal, Peter Obi, Aregbesola da manyan jagororin ADC a taron da suka yi a Abuja Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Wayas ta kuma bayyana cewa ADC na kan aikin kafa kwamitin tsare tsare da zai samar da kundin tsarin mulki ga jam’iyyar.

“Za mu kafa kwamitin tsare-tsare wanda zai fito da manufofi masu tasiri da jam’iyyar da ’yan takararta za su iya amfani da su a matsayin hanyar sake gina ƙasarmu,” in ji ta.

Rikici ya barkewa ADC ta reshen jihar Kebbi

Kara karanta wannan

Ansaru: Barnar da jagogorin yan ta'adda suka yi da ba ku sani ba kafin cafke su

A wani labarin, kun ji cewa rigima ta kaure a jam'iyyar ADC reshen jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya bayan karbar dubban masu sauya sheka.

Jiga-jigan jam'iyya sun dakatar da shugaban ADC na jihar Kebbi, Sufiyanu Bala, mataimakinsa Junaidu Muhammed da sakatariya, Hauwa Muhammed.

Ana zargi kwamitin gudanarwa da Sufiyanu ke jagoranta da yanke shawara ba tare da tuntubar shugabannin jam’iyyar ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262