Jihohi 3 da 'Yan Adawa Suka Lallasa APC a Zaben Cike Gurbi a Najeriya
A ranar asabar da ta wuce aka gudanar da zaben cike gurbi a wasu yankunan Najeriya 16, 'yan adawa sun samu nasara a kan APC a yankuna hudu.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A ranar Asabar, 16 ga Agustan 2025 hukumar zabe ta shirya zabukan cike gurbi a yankuna 16 na Najeriya.
An fafata tsakanin manyan jami'iyyun Najeriya, yayin da APC ta samu mafi yawan kujerun, 'yan adawa kuma suka samu hudu kacal.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin yankunan da 'yan adawa suka samu nasara a zaben da aka gudanar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin lura shi ne duk inda jam'iyyun hamayyar suka yi nasara, su ne ke mulkin jihohin.
1. NNPP ta kayar da APC a jihar Kano
A jihar Kano, manyan jam’iyyun siyasa guda biyu, wato NNPP da APC, sun samu kujeru ɗaya-ɗaya a zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin jiha a mazabu daban-daban.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa APC ta lashe mafi yawan zabukan cike gurbi da aka yi a Kano da jihohi 12'
A zaɓen cike gurbi na mazabar Bagwai/Shanono, jami’in tattara sakamakon zaɓe, Adamu Shitu, ya bayyana sakamakon inda ya sanar da nasarar Ali Hassan Kiyawa na jam’iyyar NNPP.
Shitu ya bayyana cewa Kiyawa ya samu ƙuri’u 16,198 inda ya kayar da abokin takararsa Ahmad Muhammad Kadamu na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’u 5,347.
An gudanar da wannan zaɓen cike gurbi ne bayan rasuwar dan majalisa Hon. Ali Ibrahim Kundila a watan Afrilu 2024.

Source: Facebook
Jam’iyyar APC ta bukaci a soke zaɓen mazabar Shanono/Bagwai da Tsanyawa/Ghari, bayan kama matasa kimanin 280 da makamai masu haɗari a rumfunan zaɓe daban-daban.
This Day ta wallafa cewa kakakin APC, Felix Morka ya ce:
“Rahotannin da za a iya tabbatarwa daga ƙananan hukumomin Shanono da Bagwai da kuma mazabar Ghari sun nuna cewa masu kada ƙuri’a sun tsere daga rumfunan zaɓe,
Yayin da jami’an tsaro da aka tura aka rinjaye su, lamarin da ya hana gudanar da zaɓe nagari mai inganci.”
2. Jam'iyyar APGA ta doke APC a Anambra
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a jihar Anambra ta ayyana Emmanuel Nwachukwu na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na Sanatan Anambra ta Kudu
Nwachukwu ya samu ƙuri’u 90,408 inda ya kayar da Azuka Okwuosa na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’u 19,812, da kuma Donald Amamgbo na jam’iyyar ADC wanda ya samu ƙuri’u 2,889.
An gudanar da zaɓen majalisar dattawa, wanda jam’iyyu 16 suka shiga, domin cike gurbin kujerar da marigayi Sanata Ifeanyi Ubah ya bari.
APGA ta sake lashe zabe a Anambra
A karo a biyu a Anambra a zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin jihar a Onitsha ta Arewa, an ayyana Ifeoma Mimi Azikiwe a matsayin wadda ta yi nasara.

Source: Twitter
Jami’in tattara sakamakon zaɓe, Farfesa Ibiam Ekpe ya bayyana cewa Azikiwe ta samu ƙuri’u 7,774 inda ta kayar Justina Azuka na jam’iyyar ADC, wadda ta samu ƙuri’u 1,909.
Punch ta wallafa cewa Justina ce matar marigayi ɗan majalisa wanda ya wakilci mazabar kafin a sace shi a daren Kirsimeti na shekarar 2024, daga baya aka gano gawarsa a cikin daji.
3. PDP ta kifar da APC a jihar Oyo
A jihar Oyo, hukumar INEC ta ayyana Folajimi Oyekunle na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na mazabar Ibadan ta Arewa a majalisar wakilai ta tarayya.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Abiodun Oluwadare daga Jami’ar Ibadan, ne ya bayyana haka a cibiyar ƙididdigar sakamako da ke Makarantar Sakandare ta Ikolaba, Ibadan.
A cewar sakamakon da INEC ta bayyana, Oyekunle ya samu ƙuri’u 18,404 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Hon. Adewale Olatunji na jam’iyyar APC, wanda ya samu ƙuri’u 8,312.

Source: Twitter
Da wannan nasara, Oyekunle zai maye gurbin marigayi ɗan majalisa Hon. Musiliu Olaide Akinremi, wanda rasuwarsa ta haifar da gurbin da ya zama dole a gudanar da zaɓen cike gurbi.
Sakamakon ya kasance babban ci gaba ga jam’iyyar PDP, inda ta sake karɓar kujerar Ibadan ta Arewa a majalisar wakilai ta tarayya karo na farko tun daga shekarar 2011.
2027: INEC ta fara rajistar masu zabe
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta sanar da fara rajistar masu zabe.
INEC ta bayyana cewa a yau Litinin, 18 ga watan Agusta na 2025 ta bude shafin rajista domin samar wa 'yan kasa katin PVC.
Bayan fara rajistar a yau ta yanar gizo, INEC ta ce a mako mai zuwa za a fara rajista kai tsaye a ofisoshinta a jihohi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

