Jagora a APC Ya Ƙaryata Zargin Ɗauke Akwatin Zaɓe a Adamawa, Ya Faɗi Abin da Ya Faru
- Mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu ya musanta satar akwatin zaɓe
- Ya bayyana cewa ba shi da dalilin da zai ɗauke BVAs kamar yadda waɗansu ke zargin ya aikata a ranar Asabar
- Mustapha Salihu, ya ce bidiyon da ke yawo da nuna cewa matasa sun zagaye motarsa ba shi da alaƙa da sace akwati
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Adamawa – Mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya karyata cewa ya yi yunƙurin sace akwatin zaɓe a Adamawa.
Bayanin ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zarginsa kwashe wasu kaya a yayin zaɓen cike gurbi na majalisar jiha a Ganye, Jihar Adamawa.

Asali: Facebook
Nigerian Tribune ta wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewa wasu fusatattun matasa sun kewaye motarsa, suna zarginsa da boye na’urar BVAS.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma sun yi zargin jagoran APC da ɓoye akwatin zaɓe a cikin motarsa,. lamarin da ya kira ƙagen siyasa.
Jagoran APC ya kare kansa kan zaben Adamawa
Sahara Reporters ta wallafa cewa Mustapa Salihu ya gudanar da taron manema labarai a Yola inda ya bayyana ainihin abin da ya faru.
Ya ce:
“Ban taba satar kayan zaɓe ba. Abin da na yi kawai shi ne shiga tsakani domin kare kayan INEC daga hannun ɓata-gari.”
Ya zargi jam’iyyar PDP da shirya tayar da tarzoma domin dakatar da ƙidaya ƙuri’u saboda ganin cewa suna shirin shan kaye.
Jagoran APC ya musanta dauke akwatin zabe
Mustapha Salihu ya ce ’yan daba sun fara tayar da tarzoma a wurin, inda ya umarci jami’an tsaro su kwantar da rikicin sannan su tabbatar cewa wakilan jam’iyyu kaɗai suka tsaya wajen sa ido.

Kara karanta wannan
PDP ta yi kuka da zaɓe a Zamfara, ta yi zargin sojoji da ƴan ta'adda sun jawo matsala

Asali: Original
Mustapha ya ce:
“Ban taɓa barin wajen da kayan zaɓe ba, kamar yadda ake zargi. Me zai sa in saci kayan zaɓe a rumfar da jam’iyyata ke samun rinjaye?”
Ya ce a rumfar zaɓe ta 06, Ganye 1 Ward, APC ta samu ƙuri’u 86, PDP kuma 36. A rumfar 010, APC ta samu 65 yayin da PDP ta samu 40.
INEC ta ce APC ta yi nasara a zaɓen Adamawa
Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta tabbatar da Musa Jauro na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbin majalisar dokokin jihar Ganye, bayan rasuwar ɗan’uwansa.
Jauro ya samu ƙuri’u 15,923, yayin da ɗan takarar PDP, Buba Muhammed Joda, ya samu 15,794 – tazara mai rauni ta ƙuri’u 129 kacal.
PDP ta zargi APC da murɗe zaɓe
A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar PDP ta jihar Zamfara ta yi watsi da zaɓen cike gurbi na Majalisar Jiha da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025.

Kara karanta wannan
APC: Duk da lashe kujera, Ministan Tinubu ya roki INEC ta soke nasarar NNPP a Kano
Shugaban PDP a jihar, Jibo Magayaki Jamilu ya kuma zargi jam’iyyar mai mulki a kasa da hada kai da sojoji da kuma 'yan bindiga wurin murɗe sakamakon zaɓen.
Ya ce jami’an tsaro sun saba wa ƙa’idojin INEC ta hanyar shiga rumfunan zaɓe, alhali ya kamata su tsaya a nesa da wuraren da aka kaɗa kuri'a don kare magudi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng