PDP Ta Yi Kuka da Zaɓe a Zamfara, Ta Yi Zargin Sojoji da Ƴan Ta'adda Sun Jawo Matsala
- Jam'iyyar PDP ta zargi APC da ke mulkin Najeriya da hada baki da sojoji wajen murɗa sakamakon zaɓen cike gurbi a Zamfa
- Ta ƙara da zargin cewa jam'iyyar ta kuma dauko hayar shugabannin ’yan bindiga don razana masu kada kuri’a a ranar Asabar
- PDP mai mulkin Zamfara ta yi gargaɗin cewa irin wannan salon da jam'iyya mai mulki a ƙasa ke amfani shi zai lalata dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara–Jam’iyyar PDP ta jihar Zamfara ta yi watsi da zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar a mazabar Kaura Namoda ta Kudu.
Ta zargi jam'iyyar ta APC da tafka maguɗin zaɓe tare da goyon bayan sojojin Najeriya da kuma ’yan bindiga a ranar 16 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan
APC: Duk da lashe kujera, Ministan Tinubu ya roki INEC ta soke nasarar NNPP a Kano

Asali: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa ƙorafin na ɗauke a jawabin Shugaban PDP na jihar, Jibo Magayaki Jamilu, ga manema labarai a Gusau ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP tana da shakku a zaɓen Zamfara
Jaridar Blueprint ta wallafa cewa Jibo ya bayyana cewa APC ta yi magudin sannan an razana masu kada kuri'a da su ka fito yin zaɓen.
PDP ta ce an hana wakilanta shiga rumfuna da cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe, wanda hakan ke nuna alamun rashin gaskiya.
Shugaban ya ce a wasu wurare ba a yi zabe ba kwata-kwata saboda razani da rashin hankali da jama'a suka shiga.
Ya ce:
"A mazabar Sakaji, babu wani zabe da aka gudanar. APC tare da sojoji suka kirkiri sakamakon ba tare da wakilanmu ba."
Jam'iyyar PDP ta zargi APC da karya doka
Ya kuma bayyana cewa an tura sojoji kai tsaye cikin rumfunan zabe a fadin mazabar, lamarin da ya saba wa dokokin hukumar zabe ta INEC.
Jibo ya ce dokokin hukumar zaɓen sun bayyana cewa jami’an tsaro su tsaya akalla mita 50 daga rumfunan da jama'a ke kada kuri’a.

Asali: Facebook
PDP ta kara da cewa shugabannin ’yan bindiga sun taimaka wajen razana da jama’a a wasu mazabun jihar.
Ya ce:
“An gargadi masu kada kuri’a cewa za a kashe su idan suka kada kuri’a ga PDP. Wannan muguwar dabara ta nuna tsananin bakin ciki da rashin tsari na APC.
PDP ta yi tir da abin da ta kira amfani da karfin gwamnatin tarayya ba bisa ka’ida ba, amma ta shawarci magoya bayanta da su kara haƙuri.
APC ta zargi NNPP ta murɗe zaɓen Kano
A baya, mun wallafa cewa Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya yi watsi da sakamakon zaɓen cike gurbi na Ɓagwai/Shanono a jihar Kano.
Da yake jawabi ga manema labarai, Ministan ya ce an tura dubunnan ’yan daban tun da safe tare da makamai, wanda ya sa al’umma gudu daga gidajensu domin su tsira da rai.
A gefe guda, jam’iyyar NNPP ta musanta zargin, inda ta ce nasarar ɗan takararta ya biyo bayan goyon bayan ɗimbin talakawan yankin da gamsuwa da salon jagorancinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng