2027: Shehu Sani Ya Ba Goodluck Jonathan Shawara kan Shigar Takarar Shugaban Kasa

2027: Shehu Sani Ya Ba Goodluck Jonathan Shawara kan Shigar Takarar Shugaban Kasa

  • Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shiga cikin masu ba Goodluck Jonathan shawara kan batun takara a zaben 2027
  • Shehu Sani ya shawarci Goodluck Jonathan da kada ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 da ake tunkara
  • Tsohon sanatan ya bayyana cewa abubuwa sun sauya sosai a jam'iyyar PDP wadda tsohon shugaban kasan ya lashe zabe a karkashinta a 2011

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ba tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, shawara kan yin takara a zaben shekarar 2027.

Shehu Sani ya shawarci Goodluck Jonathan da kada ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen 2027.

Shehu Sani ya aika sako ga Jonathan
Hoton Goodluck Jonathan yana yin jawabi a wajen taro da na Sanata Shehu Sani Hoto: @GEJonathan, @ShehuSani
Asali: Twitter

Shehu Sani, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Sunday Politics' na tashar Channels Tv, a ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan kasuwa a Arewa kuma na kusa da marigayi Shehu Shagari ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Goodluck Jonathan yana da damar takara

Goodluck Jonathan dai ya kasance mataimakin tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua na tsawon shekaru uku, kafin rasuwarsa.

Daga bisani Jonathan ya gaje shi a ranar 6 ga Mayu, 2010, har zuwa 29 ga Mayu, 2011. Daga nan kuma ya tsaya takara a karkashin PDP inda ya lashe zaɓen shugaban kasa, ya ci gaba da mulki har zuwa ranar 29 ga Mayu, 2015.

Jonathan ya sake tsayawa takara a 2015, amma ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.

A tsarin mulki, Jonathan har yanzu na da damar yin wa’adi guda na shekaru hudu idan ya so, sai dai bai nuna sha’awar sake tsayawa takarar ba.

Yayin da ake gab da zaɓen 2027, tattaunawa kan yiwuwar dawowar Jonathan ta kara ɗaukar hankalin ‘yan siyasa, musamman kasancewar ana muhawara kan batun shugaban kasa daga Kudu ya yi wa’adi daya.

Kara karanta wannan

'Zan iya soke zaɓen': Jonathan ya faɗi abin da ya kayar da shi a 2015 a hannun Buhari

Wace shawara Shehu Sani ya ba Jonathan?

Tsohon sanatan ya ce jam’iyyar PDP, wadda Jonathan ya yi amfani da ita wajen lashe zaɓen 2011, yanzu ba ta da haɗin kai kamar yadda take da shi a baya.

Shehu Sani ya ba Jonathan shawara
Hoton Shehu Sani yana jawabi a wajen wani taro Hoto: @ShehuSani
Asali: Twitter
"Duk lokacin da aka kusa yin zaɓe, sai sunan Jonathan ya taso. Amma duk da cewa dama tana hannunsa ya tsaya takara idan yana so, shawara ta gare shi ita ce kada ya yi hakan."
"Dalilin kuwa mai sauƙi ne, jam'iyyar PDP da ya sani a baya ba ita ce PDP ta yanzu ba."
“PDP ta yankin Kudu maso Yamma tana mara wa shugaban kasa baya. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar kuma suna cikin hadaka. Don haka jam’iyyar da ya sani a baya ta canza, bai kamata ya ɓata lokacinsa ba."

- Shehu Sani

Jonathan ya magantu kan zaben 2015

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya tuna baya kan abubuwan da suka faru a lokacin zaben 2015.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya riga mu gidan gaskiya

Goodluck Jonathan ya bayyana cewa an samu bambanci sosai kan yadda aka kada kuri'a yankin Arewa da Kudu, wajen yin amfani da katin tantance masu kada kuri'a.

Ya bayyana cewa da ya so, da ya soke zaben saboda yadda katin tantancewar ya rika kin yin amfani a Kudu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel