APC: Duk da Lashe Kujera, Ministan Tinubu Ya Roki INEC Ta Soke Nasarar NNPP a Kano

APC: Duk da Lashe Kujera, Ministan Tinubu Ya Roki INEC Ta Soke Nasarar NNPP a Kano

  • Jagora a APC, Yusuf Abdullahi Aya ya zargi NNPP ta kawo dubunnan ’yan daba dauke da makamai daga waje zuwa Kano
  • Aya ya bayyana cewa an yi amfani da ƴan dabam wurin razana jama'a a zaben Bagwai/Shanono da aka yi ranar Asaba
  • Ya bayyana buƙatar a gaggauta soke zaɓen, sannan a saka ranar gudanar da wani sahihi don kare mutuncin dimokuraɗiyya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi Ata ya yi watsi da sakamakon zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar a mazabar Bagwai/Shanono ta jihar Kano.

Ministan ya bayyana zaɓen a matsayin wasan kwaikwayo da ’yan daba na jam’iyyar NNPP suka mamaye wanda ya kai su ga ci.

Kara karanta wannan

PDP ta yi kuka da zaɓe a Zamfara, ta yi zargin sojoji da ƴan ta'adda sun jawo matsala

Karamin Ministan Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata
Hoton karamin Ministan Gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata Hoto: Aminu Rabi'u West/Baballe Captain
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa da yake jawabi ga ’yan jarida a Kano, Ata ya zargi NNPP da kawo ’yan daba dauke da makamai daga jihohi da ƙasashe makwabta domin razana masu kada kuri’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Tinubu ya fusata kan zaɓe a Kano

Daily Post ta ruwaito Ata ya ce duk da an rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin jam’iyyun siyasa kafin zaben, NNPP ta karya alkawarin ta hanyar tayar da tarzoma.

A kalamansa:

“Tun da 5.00 na safe a ranar zaɓe, dubunnan ƴan daba su ka mamaye yankin Bagwai da Shanono da makamai masu haɗari, ciki har da bindigu."

Ya bayyana cewa mazauna yankin da suka ga fuskoki sababbin ƴan daba sun tsere daga gidajensu saboda tsoro, inda suka nemi mafaka a Gwarzo da Bichi.

"An kai wa ɗan APC hari," Minista, Ata

Ministan ya kuma ya kara da cewa ’yan daba sun kai hari ma har gidan dan takarar APC duk domin a kawo matsala ga zaɓen.

Kara karanta wannan

Kano: Duk da lashe kujera, NNPP ta yi fatali da sakamakon zaben Ghari, Tsanyawa

Ata ya yi zargin cewa ’yan daba sun karɓe takardun kada kuri’a da na sakamako, suka cike akwatin kuri’u da sunansa, sannan suka raba kuri’un ga jam’iyyarsu ba tare da sahihin masu zabe sun kada kuri’a ba.

Ya ce:

“An hana mutanen Bagwai/Shanono, wadanda suka jima suna jiran wannan zabe tun bayan rasuwar wakilinsu, Hon. Halilu Ibrahim Kundila a watan Afrilun 2024 damar yin zabe. An tsoratar da su, an kuma kore su daga gidajensu."

Ministan ya bukaci hukumar INEC ta soke zaben, tare da saka sabon ranar gudanar da sahihin zabe mai inganci.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

Haka kuma ya roki hukumomin tsaro su gurfanar da duk wanda aka kama da hannu cikin tashin hankalin da ya faru.

Ya kuma roki magoya bayan APC da su kwantar da hankalinsu, yana jaddada cewa dole a kiyaye mutuncin tsarin zabe.

APC ta nemi INEC ta soke zaɓe a Kano

A wani labarin, mun wallafa cewa Jam'iyyar APC ta mika ƙorafin ta ga hukumar INEC, inda ta nemi a soke zaɓukan cike-gurbi a mazabun Shanono/Bagwai da kuma Ghari a jihar Kano.

Jam’iyyar ta bayyana cewa rahotanni sun tabbatar da yadda jama’a suka tsere daga rumfunan zaɓe yayin da jami’an tsaro suka kasa shawo kan rikicin da ya taso.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Felix Morka, ya ce amince wa da zaɓukan a irin wannan yanayi zai saba wa ka’idodin dimokuradiyya na gudanar da zaɓe cikin lumana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng