Kano: Duk da Lashe Kujera, NNPP Ta Yi Fatali da Zaben Ghari, Tsanyawa

Kano: Duk da Lashe Kujera, NNPP Ta Yi Fatali da Zaben Ghari, Tsanyawa

  • Jam'iyyar NNPP ta fito ta yi magana bayan ta sha kashi a hannun APC a zaben da aka gudanar na mazabar Ghari/Tsanyawa
  • Shugaban NNPP na Kano, Kwamared Hashimu Dungurawa, ya bayyana cewa an tafka magudi a zaben
  • Sai dai, ya yaba da sakamakon zaben Bagwai/Shanono wanda jam'iyyar NNPP ta samu nasarar lallasa APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta yi watsi da sakamakon zaɓen da aka sake na majalisar dokokin jiha a mazabar Ghari/Tsanyawa.

Jam'iyyar NNPP ta yi zargin akwai maguɗi da kuma haɗin baki tsakanin ‘yan siyasa da jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

NNPP ta yi fatali da sakamakon zabe a Kano
Hoton shugaban NNPP na Kano da akwatin zaben hukumar INEC Hoto: INEC Nigeria, Hashimu Dungurawa
Source: Twitter

Shugaban jam'iyyar NNPP na Kano, Kwamared Hashimu Dungurawa, ya bayyana hakan lokacin yake jawabi ga manema labarai, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tirkashi: 'Yan sanda sun cafke jami'an INEC 3, an kwato kayayyakin zabe a Taraba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar NNPP ta zargi INEC da yin magudi

Kwamared Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya zargi INEC da kin ba wa masu zaɓe hakkinsu bayan da ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara.

NNPP ta bayyana cewa zaɓen ya kamata a gudanar da shi ne a rumfunan zaɓe 10 da kotun daukaka ƙara ta soke.

Sai dai, ta zargi INEC da soke sakamakon waɗannan rumfunan sannan ta koma kan tsofaffin sakamakon da kotu ta riga ta yi fatali da su.

"A karamar hukumar Ghari, an gudanar da zaɓen lafiya a rumfunan zaɓe 10, amma ta hanyar maguɗi da wasu ‘yan siyasa marasa kishin ƙasa suka haɗa baki da jami’an INEC, aka ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya yi nasara."

- Kwamared Hashimu Dungurawa

Haka kuma jam’iyyar ta soki INEC kan yadda ta ayyana sakamakon a hedikwatar ta da ke Kano, maimakon cibiyar tattara sakamakon mazabar, tana mai cewa hakan ya ba damar yin magudi.

Kara karanta wannan

APC, PDP sun sha kashi a zaben cike gurbin Sanata Ubah da ya rasu

NNPP ta sha alwashin za ta ci gaba da adawa da abin da ta kira rashin adalci, son kai da kuma maguɗin zaɓe.

NNPP ta ki yarda da sakamakon zabe a Kano
Taswirar jihar Kano, Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

NNPP ta yaba kan zaben Shanono/Bagwai

Sai dai jam’iyyar ta yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cike gurbi na majalisar jiha a Shanono/Bagwai, inda ɗan takararta ya lashe zaɓen, tana bayyana zaben a matsayin sahihi.

Haka kuma ta gode wa jami’an tsaro bisa samar da yanayi mai kyau, tare da yabawa jama’a da suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’a.

APC ta lashe zabe a Jigawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu nasara a zaben cike gurbi da aka gudanar na mazabar Garki/Babura a jihar Jigawa.

Dan takarar APC, Alhaji Rabiu Mukhtar, ya lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Auwalu Isah Manzo.

An dai gudanar da zaben ne a ranar Asabar, 17 ga watan Agustan 2025 domin cike gurbin marigayi Hon. Isa Yaro, wanda ya rasu a cikin watan Mayun shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng