Duk da Tasirin El Rufai, APC Ta Lashe Zaben Cike Gurbi da Tazara Mai Yawa a Kaduna
- A jihar Kaduna, ɗan takarar APC Felix Joseph Bagudu ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Chikun–Kajuru da kuri’u 34,580
- Farfesa Abubakar Jumare na INEC ya bayyana sakamakon, inda ya ce Bagudu ya doke PDP wacce ta samu kuri’u 11,491
- Sakamakon ya ƙara tabbatar da rinjayen APC a Kaduna, yayin da jam’iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC ta samu kuri'u 3,477
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - An ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Felix Joseph Bagudu a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbin kujerar majalisar wakilai na Chikun–Kajuru a jihar Kaduna.
Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Abubakar Jumare, ya ayyana Bagudu a matsayin zakara bayan ya samu jimillar kuri’u 34,580 a kananan hukumomi biyu na mazabar.

Asali: Twitter
APC ta lashe zaben cike gurbi a Kaduna

Kara karanta wannan
Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar Jigawa da ya rasu
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Farfesa Abubakar Jumare ya ayyana sakamakon zaben ne a ranar Lahadi bayan jami'an zaben kananan hukumomin sun gabatar da sakamakon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da dan takarar APC Felix Bagudu ya samu kuri'u 34,580, abokiyar hamayyarsa, Princess Esther Ashivelli Dawaki ta jam’iyyar PDP, ta samu kuri’u 11,491, lamarin da ya bar tazarar kuri’u 23,089 a tsakaninsu.
A karamar hukumar Kajuru, APC ta samu kuri’u 10,487 yayin da PDP ta samu 6,789, sai kuma a karamar hukumar Chikun, jam’iyyar mai mulki ta samu kuri’u 24,093, PDP kuma ta samu kuri’u 4,702.
Jam’iyyar ADC ta zo ta uku da tazara mai nisa inda ta samu kuri’u 3,477 a kananan hukumomi biyun, sauran jam’iyyu kuma suka samu mafi karancin kuri'u.
Jam'iyyar APC ce mai nasara a Kaduna
Farfesa Jumare, wanda ya bayyana sakamakon ƙarshe a cibiyar tattara sakamakon, ya ce an fafata sosai a zaben, amma an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali a mazabu biyun.

Kara karanta wannan
APC ta sha kasa a zaben cike gurbi, PDP ta kwato kujerar majalisar wakilai a Ibadan
Da wannan nasarar, Bagudu zai cike gurbin da ya bayyana a majalisar wakilai na tarayya daga mazabar, bayan rasuwar ɗan majalisar jam’iyyar LP, Ekene Abubakar Adam.
Sakamakon zaben cike gurbin da aka gudanar a ranar Asabar ya ƙara tabbatar da rinjayen jam’iyyar APC a siyasar Kaduna.

Asali: Twitter
Kaduna: APC ta yi nasara a Zaria, Basawa
Hakan na zuwa ne bayan APC ta lashe kujerar mazabar Zaria Kewaye, inda jami’in tattara sakamakon, Farfesa Balarabe Abdullahi, ya bayyana cewa ɗan takarar APC, Isa Haruna Ihamo ya samu kuri’u 26,613, inji rahoton Vanguard.
Abdullahi ya ƙara da cewa ɗan takarar jam’iyyar SDP, Nuhu Sada Abdullahi ya samu kuri’u 5,721, yayin da ɗan takarar PDP, Mamuda Abdullahi Wappa ya samu kuri’u 5,331.
Haka zalika, hukumar INEC ta ayyana Alhaji Dahiru Umar-Sani na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe kujerar mazabar Basawa a majalisar dokokin jihar Kaduna.
Farfesa Nasiru Rabiu daga jami’ar Ahmadu Bello Zaria (ABU), ya ce Umar-Sani ya samu kuri’u 10,996 inda ya doke abokin hamayyarsa, Muazu Danyaro na PDP, wanda ya samu kuri’u 5,499.

Kara karanta wannan
ADC, PDP sun kwashi kashinsu a hannu, APC ta lashe zabe da tazara mai yawa a Ogun
APC ta karyata ADC kan murdiyar zabe
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kaduna ta karyata zargin da jam’iyyun ADC da SDP na cewa tana shirin tafka maguɗin zaɓe a zaɓukan cike-gurbi.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya bayyana zargin jam'iyyun adawar a matsayin marar tushe kuma cike da makirci.
Ya ce gwamnati ba ta da wani hurumi wajen gudanar da zaɓe saboda aikin hukumar INEC ne kawai, tare da gargadin cewa gwamnati ba za ta zauna lafiya a ci gaba da ɓata sunanta ba.
Asali: Legit.ng