APC Ta Sha Kasa a Zaben Cike Gurbi, PDP Ta Kwato Kujerar Majalisar Wakilai a Ibadan
- PDP ta samu babban nasara yayin da INEC ta ayyana Folajinmi Oyekunle a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Ibadan ta Arewa
- Farfesa Abiodun Oluwadare na jami’ar Ibadan ya tabbatar da sakamakon, inda PDP ta samu kuri’u 18,404, sao APC ta samu kuri’u 8,312
- Wannan nasara ta PDP ta dawo musu da kujerar da suka rasa tun 2011, kuma ta maye gurbin marigayi Musiliu Akinremi (Jagaban)
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Folajinmi Oyekunle, a matsayin wanda ya lashe zaben Ibadan ta Arewa.
INEC ta ce Folajinmi Oyekunle ne ya lashe zaben cike gurbi na kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ibadan ta Arewa North da aka gudanar a ranar Asabar.

Kara karanta wannan
ADC, PDP sun kwashi kashinsu a hannu, APC ta lashe zabe da tazara mai yawa a Ogun

Source: Twitter
PDP ta lashe zabe a Ibadan ta Arewa
Jami’in tattara sakamakon zaben na INEC, Farfesa Abiodun Oluwadare daga jami’ar Ibadan, ne ya sanar da sakamakon a makarantar sakandare ta Ikolaba, Ibadan, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa Oyekunle ya samu kuri’u 18,404 inda ya doke dan takarar APC, Adewale Olatunji da aka fi sani da Murphy, wanda ya samu kuri’u 8,312 kacal.
Oluwadare ya kara da cewa Femi Akin-Alamu na jam’iyyar ADC ya samu kuri’u 88, yayin da Olabisi Olajumoke na jam’iyyar APGA ya samu kuri’u 40.
Haka kuma ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar ZLP, Hammed Badmus, ya samu kuri’u 18 ne kawai.
PDP ta yi babban nasara karo na farko
An rahoto Farfesa Oluwadare yana cewa:
“Wannan shi ne sakamakon. Ni, Farfesa Abiodun Oluwadare, na tabbatar cewa ni ne jami’in tattara sakamakon zaben cike gurbi na majalisar wakilai na Ibadan ta Arewa da aka gudanar a ranar 16 ga watan Agusta, 2024.
“Na ayyana cewa Folajinmi Oyekunle na jam’iyyar PDP, kasancewar ya cika sharuddan doka, ya zama zakaran zaben da aka gudanar."
Da wannan nasara, Oyekunle zai maye gurbin kujerar marigayi dan majalisar, Musiliu Akinremi, wanda aka fi sani da Jagaban, wanda rasuwarsa ta haifar da gurbi da kuma bukatar wannan zaben cike gurbi.
Sakamakon ya kasance babban ci gaba ga PDP, domin ya nuna nasarar jam’iyyar wajen sake kwato kujerar mazabar Ibadan ta Arewa a karo na farko tun shekarar 2011.

Source: Twitter
Abin da gwamna ya ce kafin nasarar PDP
Jaridar The Cable ta rahoto cewa a ranar 5 ga watan Agusta, 2025, gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya ce nasarar PDP a wannan zabe za ta kara tabbatar da rinjayen jam’iyyar a jihar.
Gwamnan Seyi Makinde, wanda ya yi jawabi a kasuwar Bodija da ke Ibadan yayin kaddamar da yakin neman zaben PDP, ya bayyana Oyekunle a matsayin “amintacce, ƙwararre, kuma mafi dacewa don wakiltar” mazabar a majalisar wakilai.
APC ta lashe zabe a mazabar Remo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yar takarar jam’iyyar APC, Adesola Ayoola-Elegbeji, ta yi nasara a zaben cike gurbi bayan ta lashe kuri’u mafi rinjaye a Ogun.

Kara karanta wannan
Babu labarin Fintiri da Atiku, INEC ta sanar da sakamakon zaɓen cike gurbi a Adamawa
Hukumar INEC ta ce Ayoola-Elegbeji ta samu kuri’u 41,237 inda ta doke abokiyar hamayyarta Bola Oluwole ta PDP don zama 'yar majalisar mazabar Remo.
Bayan nasararta, Misis Adesola Ayoola-Elegbeji ta yi godiya ga al’umma tare da yin alkawarin samar da ayyukan yi ga matasa da mata da ababen more rayuwa.
Asali: Legit.ng
