ADC, PDP Sun Kwashi Kashinsu a Hannu, APC Ta Lashe Zabe da Tazara Mai Yawa a Ogun
- A jihar Ogun, ‘yar takarar jam’iyyar APC, Adesola Ayoola-Elegbeji, ta yi nasara a zaben cike gurbi bayan ta lashe kuri’u mafi rinjaye
- Hukumar INEC ta ce Ayoola-Elegbeji ta samu kuri’u 41,237 inda ta doke abokiyar hamayyarta Bola Oluwole ta PDP
- Bayan nasararta, Ayoola-Elegbeji ta yi godiya ga al’umma tare da yin alkawarin samar da ayyukan yi da ababen more rayuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun - ‘Yar takarar jam’iyyar APC, Misis Adesola Ayoola-Elegbeji, ta zama zakara a zaben cike gurbi na majalisar wakilai da aka gudanar a ranar Asabar.
Misis Adesola Ayoola-Elegbeji, ta lashe zaben ne domin wakiltar mazabar Remo da ke jihar Ogun a majalisar tarayya.

Asali: UGC
'Yar takarar APC ta lashe zabe a Ogun
Premium Times ta rahoto cewa Ayoola-Elegbeji ta yi nasara a dukkanin kananan hukumomin uku na Sagamu, Ikenne da kuma Remo ta Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Kazeem Bello, ne ya bayyana sakamakon da safiyar Lahadi a cibiyar tattara sakamakon hukumar INEC da ke Ikenne.
Farfesa Bello ya bayyana cewa ‘yar takarar APC ta lashe zaben bayan ta samu kuri’u 41,237, inda ta doke abokin hamayyarta mafi kusa, Bola Oluwole ta jam’iyyar PDP, wadda ta samu kuri'u 14,324. Jam’iyyar ADC ta samu kuri’u 289 kacal.
Ogun: Sakamakon zaben mazabar Remo
- Karamar hukumar Ikenne
Masu kada kuri'a da aka tantance: 17,477
APC – 10,227
PDP – 5,595
ADC – 73
- Karamar hukumar Remo ta Arewa
Masu kada kuri'a da aka tantance: 9,374
APC – 8,052
PDP – 992
ADC – 37
- Karamar hukumar Sagamu
Masu kada kuri'a da aka tantance: 32,574
APC – 22,958
PDP – 7,737
ADC – 179
Abin da INEC ta ce kan zaben Ogun
Yayin bayyana sakamakon ƙarshe na zaben, Farfesa Bello ya ce:

Kara karanta wannan
Babu labarin Fintiri da Atiku, INEC ta sanar da sakamakon zaɓen cike gurbi a Adamawa
“’Yar takarar APC, Adesola Ayoola-Elegbeji, kasancewar ta cika duk sharuddan dokar zabe tare da samun mafi yawan kuri’u, an ayyana ta a matsayin zakarar zaben cike gurbi don maye gurbin kujerar mazabar Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa a majalisar wakilan tarayya.”
Sauran jami’an tattara sakamakon zaben da suka taka rawa sun haɗa da Farfesa Richard Abayomi Sobayo (Sagamu), Dakta Akeem Adekunle Makinde (Ikenne), da Dakta Matthew Wheto (Remo North).

Asali: Twitter
Godiyar 'yar takarar APC da sabon alkawari
Bayan sanar da nasararta, Ayoola-Elegbeji ta yi godiya ga al’ummar mazabar Remo bisa irin amincewar da suka nuna mata, inji rahoton Punch.
Ta yi alkawarin yin wakilci na gaskiya, tare da dorawa daga manyan ayyukan da tsohuwar 'yar majalisar mazabar, marigayiya Misis Adewunmi Onanuga (Ijaya), ta fara aiwatarwa kafin rasuwarta a ranar 15 ga Janairu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ayoola-Elegbeji ta kuma sha alwashin mayar da hankali kan inganta matasa, samar da ayyukan yi da sabunta ababen more rayuwa domin inganta rayuwar jama’ar mazabarta.
Dan takarar NNPP ya lashe zabe a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, INEC ta kammala tattara kuri'un da aka kada a zaben cike gurbin dan Majalisar Shanono/Bagwai a Kano.
Dan takarar NNPP, Ali Lawan Alhassan ne ya samu nasara da kuri'u mafi rinjaye a zaben da aka gudanar jiya Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025.
A sakamakon da INEC ta sanar, NNPP mai mulki ta samu kuri'u 16,198 yayin da jam'iyyar adawa watau APC ta samu kuri'u 5347.
Asali: Legit.ng