Rigima Ta Barke a Zaben Cike Gurbin Sanata Ubah da Ya Rasu, An Kama 'Yan APC
- Sanata Ifeanyi Ubah, wanda ya rasu a watannin baya na daya daga cikin yan majalisar tarayya da ake gudanar da zaben cike gurbinau yau Asabar
- Rahotanni sun nuna cewa rikice-rikice sun mamaye rumfunan zabe da dama a zaben maye gurbin sanatan Anambra ta Kudu
- Jami'an tsaro da suka hada da yan sanda sun shiga tsakani domin kwantar da hankula da ci gaba da kada kuri'a a rumfunan da abin ya shafa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Rahotanni sun nuna cewa rigingimu da zanga-zanga sun mamaye zaben cike gurbin Sanatan Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah wanda ya rasu.
Zaben maye gurbin Sanata Ubah na daya daga cikin zabukan da hukumar zabe ta kasa watau INEC ta gudanar a yau Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta tattaro cewa zaben na yau a mazabar Anambra ta Kudu cike yake da rikici da tarzoma, lamarin da ya kai ga kama wasu ’yan jam’iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama wakilan dan takarar APC a Anambra
Bayanai sun nuna cewa an kama wakilan rumfunan zaɓe huɗu na ɗan takarar jam'iyyar APC, Sir Azuka Okwuosa.
Shugaban ƙaramar hukumar Ekwusigo, tare da goyon bayan wani shugaban al’umma a Ozubulu ne suka jagoranci kama mambobin na APC.
Wannan lamari ya sa wasu matasa a yankin suka fantsama zanga-zanga bisa zargin gwamnatin Anambra ta jam’iyyar APGA da cin zarafi da razanarwa ga 'yan adawa
Rikici ya mamaye zaben Anambra ta Kudu
Tsohuwar kakakin majalisar dokokin Anambra, Hon. Rita Maduagwu, ta shaida wa jaridar Punch cewa APGA ta mamaye mazabar ta a Ukpor Ward 3, 009 domin tayar da tarzoma ga masu kada kuri’a.
Bugu da kari, hakan ya ƙara haifar da zaman dar-dar da tashin hankali a kananan hukumomin Nnewi da Ekwusigo.

Kara karanta wannan
Trump na neman kawo hari Najeriya, an jibge jami'an tsaro 60000 domin zaben Anambra
Wasu wuraren da aka samu tashin hankali sun haɗa da Ward 4, Units 001 da 003, da kuma Ward 4, Unit 8 a Ekwusigo, inda jami’an gwamnati suka kama wakilan APC suka tafi da su.

Source: Twitter
Jami'an tsaro sun dauki mataki
Tuni dai jami’an tsaro suka yi kokarin shiga tsakani domin shawo kan lamarin a duka wuraren da rigima ta barke.
Sai dai kuma, Sakataren Yaɗa Labarai na APGA ta kasa, Ejiomofor Opara, ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa babu wani dan jam'iyya ko jami'in gwamnatin Anambra da zai aikata hakan.
Mista Opara Ya zargi ’yan APC da ƙirƙirar labarin tashin hankali da kame don su dauke hankalin mutane.
An kama wakilin PDP da kusan N26m
Kuna da labarin yan sanda da jami'an DSS sun cafke wani mutumi da ake zargin wakilin PDP ne dauke da kudi kusan miliyan 26 a jihar Kaduna.
Ana zargin cewa mutumin wakilin PDP ne kuma zai yi amfani da wadannan kudade wajen sayan ƙuri’u a zaben cike gurbin da ake yi a Chikun/Kajuru.
Rahotanni sun ce dan PDP ya shiga hannu ne a daidai lokacin da yake tsara yadda za a rarraba kuɗin da aka tanada ga abokan aikinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
