APC Ta Tsorata, Ta Bukaci INEC Ta Soke duka Zaben Cike Gurbi a Kano
- Jam'iyyar APC ta buƙaci INEC ta soke zaɓukan cike gurbi a Shanono/Bagwai da Ghari saboda tashin hankali
- Ta ce rahotanni sun nuna jama’a sun gudu daga rumfunan zabe, jami’an tsaro kuma sun gagara shawo kan rikicin
- Jam’iyyar ta ce gudanar da zaɓen cikin irin wannan yanayi barazana ce ga tsarin dimokuradiyya a Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyya mai mulki a Najeriya, APC ta miƙa kokenta ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kan zaɓen cike gurbi a Kano.
APC ta bayyana cewa a akwai damuwa, saboda haka ya roƙi INEC ta soke zaɓen majalisar dokokin jihar Kano a mazabar Bagwai/Shanono da kuma sake zaben da ake gudanarwa a mazabar Ghari.

Asali: Facebook
A sakon da APC ta wallafa a shafinta na X, ta ce ba a gudanar da zaɓen a cikin lumana ba, saboda haka akwai bukatar INEC ta ɗauki mataki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce an samu tashin hankali, rikici, da kuma fitinar ’yan daba a rumfunan zabe daban-daban a mazabun da abin ya shafa.
APC ba ta gamsu da zaɓen Kano ba
APC ta ce akwai sahihan bayanai daga Shanono, Bagwai da Ghari da suka tabbatar da cewa jama’a sun gudu daga rumfunan zabe saboda rikicin da ya barke.
Sanarwar da Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Felix Morka ya sanya wa hannu ta ce har jami’an tsaro da aka tura wuraren sun kasa shawo kan rashin hankalin.

Asali: Twitter
Jam’iyyar ta yi nuni da cewa irin wannan yanayi ya sa babu yiwuwar gudanar da sahihin zabe a wuraren da ake magana a kai.
A cewar jam’iyyar, ci gaba da gudanar da irin wannan zabe a yanayin tsoratarwa da cin zarafin masu kada kuri’a zai sabawa ƙa’idodin dimokuradiyya.
Jam'iyyar APC ta shiga damuwa kan zaben Kano
Jam'iyyar APC ta ce ci gaba da zaɓe a Kano na iya kafa wani mummunan misali da zai haifar da barazana ga tsarin zabe a nan gaba.
Sanarwar Felix Morka ta ce:
"Rahotanni tabbatattu sun nuna cewa masu kaɗa kuri’a na tserewa daga rumfunan zabe, yayin da jami’an tsaro da aka tura suka gagara shawo kan tashin hankalin, lamarin da ya sanya yiwuwar gudanar da zabe na gaskiya da sahihanci ya zama abin wuya."
Jam’iyyar ta ce gudanar da zaben cikin irin wannan yanayi barazana ce ga tsarin dimokuradiyya.
APC ta ce:
"Ci gaba da gudanar da zaɓen cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma zaɓen maimaitawa na Ghari a cikin yanayin ta’addancin ’yan daba da tsoratar ga masu kaɗa kuri’a zai zama sabawa ƙa’idojin dimokuraɗiyya na gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci da lumana."
Irinsu Ibrahim Adam wanda hadimi ne ga gwamnan Kano, ya fito shafin Facebook yana cewa wannan shi ne zaben cike-gurbi mafi aminci a jihar.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama wakilin PDP a otal dauke da kusan Naira miliyan 26 a Kaduna
Mai ba gwamna Abba Kabir shawaran ya yi ikirarin ba a taba zabe na cike gurbi wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali irin na wannan karo ba.
Ƴan daba sun shiga hannu a Kano
A baya, kun ji cewa Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tabbatar da kama sama da mutum 100 da ake zargin ‘yan daba ne ana cikin zabe a Kano.
Kwamkshinan hukumar reshen jihar Kano, Abdu Zango ya ce an kama su Bagwai, yayin da ake gudanar da zaɓen cike-gurbin dan majalisar jihar yankin.
Abdu Zango ya kuma bayyana cewa duk da rahotannin ‘yan daban da makamai sun bayyana a wasu rumfunan zaɓen, komai ya ci gaba da tafiya a cikin lumana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng