Ana Zargin Sukar Gwamnati Ta Jawo Kai Hari kan Jigon APC, Ya Sha da Ƙyar a Abuja

Ana Zargin Sukar Gwamnati Ta Jawo Kai Hari kan Jigon APC, Ya Sha da Ƙyar a Abuja

  • Tsohon dan takarar gwamna na Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya tsallake yunƙurin kashe shi a birnin Abuja
  • Shinkafi ya ce ‘yan bindiga masu sanye bakaken kaya da makamai sun tare motarsa, suka kai masa hari
  • Ya danganta harin da matsayinsa kan tsaro da suka jawo barazana, inda ya bukaci hukumomi su ɗauki mataki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wani jigo na jam’iyyar APC kuma tsohon dan takarar gwamna a Zamfara ya tsallake rijiya da baya a Abuja.

Dr. Sani Shinkafi, ya tsallake yunƙurin kashe shi a Abuja ranar Juma’a 15 ga Agusta, 2025.

Miyagu sun kai hari kan jigon APC a Abuja
Dr. Sani Shinkafi yana yawan sukar gwamnati kan rashin tsaro. Hoto: Dr. Sani Abdullahi Shinkafi.
Source: Facebook

Jigon APC ya sha da kyar a Abuja

Shinkafi ya bayyana cewa harin ya auku ne jim kadan bayan sallar Juma’a a hanyarsa ta dawowa gida, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan kasuwa a Arewa kuma na kusa da marigayi Shehu Shagari ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi suka ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan sallar Juma'a inda wasu suka tare shi da makamai a Abuja da ke tsakiyar Najeriya.

Shinkafi ya ce maharan sanye bakaken kaya, dauke da manyan makamai, sun tare motarsa kafin su kai masa hari, sannan suka tsere da bakar mota kirar Prado.

Lamarin ya haifar da damuwa saboda barazanar da ake ta fuskanta daga ‘yan ta’adda da kuma yadda ake kai hari ga fitattun mutane a kasa.

Kungiyar 'Patriots for the Advancement of Peace and Social Development' ta ce yunƙurin kashe shi ya biyo bayan tsayin daka kan batutuwan tsaro a Zamfara.

“Wannan kokari ne na ganin baya na, amma ba zan bari barazana ta hana ni magana kan tsaro, zaman lafiya da cigaba ba.”

- Cewar Shinkafi

Shinkafi ya bayyana cewa gidansa a Abuja ya rika samun kiran barazana a makon da ya gabata, kuma yana da alaka da wannan hari.

Kara karanta wannan

Wata 1 da rasuwar Buhari, ma'aikatansa sun yi hawaye, sun fadi kyawawan halayensa

Shinkafi ya roki alfarma wurin yan sanda
Babban Sufeto- Janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Shinkafi ya roki alfarma wurin yan sanda

Ya roki Sufeto Janar na ‘yan sanda da Darakta Janar na DSS su binciki lamarin, su gano masu hannu, sannan su hukunta su.

Shinkafi ya jima yana sukar matsalar ta’addanci da satar mutane a Zamfara, inda yake shawartar iyalai ka da su biya kudin fansa.

Ya ce yana yawan kiran tsaurara matakai kan tsaro a Najeriya, yana mai cewa hakan ya zama wajibi don tsaro da dimokradiyya, Daily Post ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa tsaro yana da muhimmanci wajen tabbatar da cigaban kasa da kuma nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.

Sai dai har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da wannan mummunan hari da aka kai wa Shinkafi a Abuja.

Shinkafi ya koka kan matsalar tsaro a Arewa

Mun ba ku labarin cewa Kungiyar PAPSD ta nemi gwamnonin Arewa maso Yamma da su magance rashin tsaro ta hanyar inganta ilimi da ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gaji da hare hare, ya roki Allah game da masu daukar nauyin ta'addanci

Kungiyar ta ce saka hannun jari a fannin ilimi, noma, da walwalar jama’a na taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro.

Dr Sani Abdullahi Shinkafi, shugaban PAPSD ya ba da shawarar a yanke hukuncin kisa ga 'yan fashi da masu aikata ta'addanci a kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.