Bayan Fitowa daga Komar EFCC, Tambuwal Ya Sha Alwashi kan Gwamnatin APC
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi maganganu bayan ya fito daga komar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC)
- Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu ya bayyana cewa dole ne a hada karfi da karfe wajen fatattakar jam'iyyar APC daga kan mulki
- Ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da APC sun jefa 'yan Najeriya cikin wani mawuyacin hali
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal, a ranar Juma’a ya shiga birnin jihar.
Tambuwal ya samu tarba cikin gagarumin biki daga magoya bayansa na jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce dawowar tsohon kakakin majalisar wakilan ta jawo dubban mambobin jam’iyya, kungiyoyin mata, kungiyoyin matasa da magoya baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dubban mutane sun tarbi Aminu Tambuwal
Mutanen sun cika tituna suna raira wakokin nuna goyon baya ɗauke da tutoci da manyan alluna da ke nuna shirin kwace mulki daga jam’iyyar APC mai mulki.
Yayin da yake jawabi ga taron mutanen, Tambuwal, wanda ya jagoranci kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a lokacin zaɓen 2023, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin APC,
Tambuwal ya zarge su da jefa Najeriya cikin matsanancin kuncin tattalin arziki, rashin tsaro da durkushewar siyasa.
“A 2023, mun zagaya faɗin kasar nan muna gargadin ‘yan Najeriya kada su zaɓi Bola Ahmed Tinubu, mutumin da jagorancinsa zai jefa kasar nan cikin abin da na kira (Sharar Bola)."
"Kuma yau, wahala, yunwa da rashin fata da kuke gani a ko ina shaida ce ta abin da muka faɗa."
- Aminu Waziri Tambuwal
Tambuwal ya shawarci 'yan Najeriya kan APC
Ya kira ga ‘yan Najeriya daga kowane yanki da su haɗa kai su shirya don kifar da Tinubu da APC daga mulki a 2027, yana mai jaddada cewa gwamnatin yanzu ba ta da abin da za ta iya bayarwa face kara jefa jama’a cikin wahala.

Asali: Facebook
"Sakon da nake da shi mai sauki ne, dole mu haɗa karfi mu kori APC da Tinubu a 2027. ADC tare da abokan tafiyarmu za mu tashi tsaye mu wayar da kan al’umma a kowane sashi na kasar nan domin cimma hakan."
"Ba za mu bari a tsoratar da mu ba, ba za mu bari a kakaba mana yin shiru ba, kuma ba za mu bari wahalar ‘yan Najeriya ta ci gaba ba."
- Aminu Waziri Tambuwal
Naja'atu Muhammad ta ziyarci Tambuwal
A wani labarin kuma, kun ji cewa fitacciyar 'yar gwagwarmaya kuma 'yar siyasa . Arewacin Najeriya, Hajiya Naja'atu Bala Muhamamad ta kai ziyara ga tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.
Naja'atu ta bayyana cewa sun kai wa Tambuwal ziyarar ne don karfafa masa gwiwa biyon bayan kamun da hukumar EFCC ta yi masa.
Ta bayyana cewa sun kuma yi masa jaje tare da taya shi murna bayan ya shaki iskar 'yanci sakamakon tsare shi da EFCC ta yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng