An Dauko Batun Wanda Za a Nada a Matsayin Sabon Shugaban INEC kafin Zaben 2027
- A karshen shekarar 2025, wa'adin shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu zai kare
- Bisa tanadin kundin tsarin mulki, shugaban kasa ne ke da ikon nada shugaban INEC, sannan Majalisar Tarayya ta tantance shi
- Kungiyar Yiaga Africa ta bai wa Shugaba Bola Tinubu shawarwarar wanda ya kamata ya nemo, ya ba shi wannan aiki mai muhimmanci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kungiyar Yiaga Africa, ta shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya naɗa ƙwararre a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
Ta kuma bukaci shugaban kasa ya lalubo mutane masu nagarta ya nada su a matsayin kwamishinonin INEC, wadanda ke jagorantar harkokin zabe a jihohi.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wa’adin mulkin shugaban INEC na yanzu, Farfesa Mahmood Yakubu, zai ƙare a ƙarshen wannan shekara da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara ba Tinubu shawara kan kujerar INEC
Yiaga Africa ta bukaci Shugaba Tinubu da ya nemo mutane masu ƙwarewa da nagarta, wadanda ba su dogara da kowa ba, ya ba su shugabancin hukumar INEC.
Kungiyar ta bayyana haka ne a wani taron tattaunawa da aka shirya kan kare ’yancin hukumar INEC wanda ya gudana a ranar Juma’a a Abuja,
Babban Daraktan Yiaga Africa, Samson Itodo, ya yi gargadin cewa naɗin shugabanni ba tare da zurfin tunani ba na iya raunana hukumar zaɓe kuma ya lalata dimokuraɗiyyar Najeriya.
'Wadanda ya kamata a nada su jagoranci INEC'
Itodo ya jaddada cewa dole a kula sosai wajen sauyin shugabanci da ke tafe a INEC domin kada a dakushe hukumar wajen gudanar da ingantattun zaɓe.
“Ba wai kawai cika sharuddan kundin tsarin mulki na kasancewa mutum mai gaskiya da rashin son kai kadai ake so ba.

Kara karanta wannan
Jerin sunaye: Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'i 9 a Kaduna da wasu jihohi 7
"Muna bukatar mutanen da suka nuna ƙwarewa wajen gudanar da zaɓe, basira, fasaha, kuzari, da ƙarfin hali wajen kauce wa matsin lamba na siyasa," in ji shi.

Asali: Facebook
Yiaga Africa ta fadi tsarin da ya kamata a bi
Ya shawarci shugaban ƙasa da ya tabbatar da gaskiya a tsarin naɗa shugabannin INEC ta hanyar bayyana sunayen waɗanda ake son naɗawa kafin a tura su majalisar dokoki ta ƙasa.
Itodo ya bayar da shawarar a bai wa ’yan ƙasa, kungiyoyin farar hula, da ƙwararru damar duba da kuma miƙa ƙorafe-ƙorafe kan jerin sunayen waɗanda aka zaɓa.
Ya bayyana cewa irin waɗannan matakai za su ƙara wa jama’a kwarin gwiwa kuma su taimaka wajen tabbatar da sahihancin babban zaɓen 2027 wanda yanzu saura kwanaki 554, rahoton Premium Times.
INEC za ta fara rijistar masu kada kuri'a
A wani labarin, kun ji cewa hukumar zabe mai ta kasa watau INEC za ta fara rijistar masu kada kuri’a ta yanar gizo a ranar 18 ga watan Agusta, 2025.
INEC ta bayyana cewa rijistar za ta kasance wani mataki na farko a cikin shirye-shiryen da ake yi na gudanar da zaben gwamna a Jihar Anambra da zaben 2027.
A cewa INEC, ta kuduri aniyar karfafa hadin gwiwa da kungiyoyin fararen hula, jam’iyyu da kafafen yada labarai domin karfafa shiga harkokin zabe musamman ga matasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng