'Yan Takara 2 da Gwamna Abba Ya Roki Mutanen Kananan Hukumomi 4 Su Zaba a Kano
- Gwamna Abba Kabir ya halarci kamfen NNPP gabanin zaben cike gurbin da za a yi a mazabun 'yan Majalisar Dokokin Kano guda biyu
- A gobe, Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025, hukumar INEC ta shirya zaben cike gurbi a mazabun Shanono/Bagwai da Ghari/Tsanyawa
- A wurin kamfen, Gwamna Abba ya bayyana wasu daga cikin masarorin da gwamnatinsa ta samu a yankin cikin shekaru biyu a kan mulki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya yi kira ga mazauna kananan hukumomin Ghari, Tsanyawa, Bagwai, da Shanono su zabi NNPP a zaben cike gurbin da za a yi gobe Asabar.
Gwamna Abba ya bukaci jama'ar mazabun su yi nazari kan nasarorin da jam’iyyar NNPP ta samu a cikin shekaru biyu da suka gabata kafin su kada kuri’arsu.

Source: Twitter
Abba ya yi wannan furucin ne a wurin gangamin kamfen NNPP a mazabun yan majalisar dokoki biyu da za a cika zabensu gobe Asabar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya fadi wasu nasarorin NNPP
A kamfen NNPP daya halarta a ranar Alhamis, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta yi namijin kokari wajen inganta bangarorin kiwon lafiya, ilimi, da ci gaban dan Adam.
"A cikin shekaru biyu da muka zo, mun gina ajujuwa da dama, mun dauki nauyin ɗaruruwan matasa domin ci gaba da karatu a cikin gida da kasashen waje.
"Sannan mun bai wa dubban mata tallafin kuɗin fara sana’a na N50,000 duk wata. Duka wadannan kokari don inganta rayuwar al’ummar wadannan mazabu ne.”
- In ji Gwamna Abba.
Gwamna Abba ya gargadi mutanen mazabun
Ya gargadi jama’a kada su koma ga abin da ya kira “mummunan mulki da sakaci” na gwamnatin da ta gabata.

Kara karanta wannan
Zabe ya dauki zafi, ana zargin an sace yar takarar majalisar tarayya da wasu 25 a Kaduna
"Yanzu sun dawo suna neman kuri’unku. Ina da tabbacin ba za ku zabi wadannan makiyan jiharmu ba.”
Gwamna Abba Yusuf ya kuma bayyana cewa kasafin kudin jihar na 2025 ya tanadi gina babbar hanya da za ta hada Mashatsa–Gwarzo–Shanono–Tanyawa.
Ya ce za kuma a daga darajar Asibitin Shanono zuwa babban Asibiti, tare da shimfida bututun ruwa daga wani dam a kusa domin samar da ruwan sha mai tsafta ga al’ummar mazabar.

Source: Twitter
'Yan takara 2 da Gwamna ya nemi a zaba
Abba Kabir ya roki jama'a su kada kuri’un su ga Ali Kiyawa a matsayin dan Majalisar Bagwai/Shanono da Yusuf Maigado a matsayin dan majalisar Ghari/Tanyawa.
Gwamnan ya bukaci masu katin zabe a wadannan mazabu su fito kwansu da kwarkwata a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025, su zabi yan takarar jam'iyyar NNPP.
Bugu da kari, ya shawarci matasa masu shekaru 18 zuwa sama da ba su da katin zabe watau PVC su tabbata sun yi rajistar masu kada kuri’a da za a fara nan ba da jimawa ba.
Wani dan Kwankwasiyya a Kano, Malam Sanusi Isyaku ya shaidawa Legit Hausa da kwarin guiwarsa cewa NNPP ce za ta lashe zabukan cike gurbi.
"Ka duba dandazon al'ummar da suka zo wurin tarbar Abba da wadanda suka halarci taron kamfe, kai ka san cewa ana son NNPP ko nace maka Kwankwaso da Abba.
"Mutanen Kano ba za su kara yarda da wadancan mutanen ba, muna fatan dai a yi zabe cikin lumana a gobe Asabar," in ji shi.
Kwankwaso ya karbi masu sauya sheka zuwa NNPP
A wani labarin, kun ji cewa jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Kwankwaso ya karbi wasu yan APC da suka sauya sheka a jihar Kano.
Ya ce tsarin shugabanci a jihar Kano da irin sahihin jagorancin siyasa da suke da shi ne ke janyo mutane su shiga NNPP.
Kwankwaso ya kara samun dumbin magoya baya ne yayin da ake rade-radin cewa Shugaba Tinubu na son ya dawo jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

