'Na Tsine wa Gwamnatin Uba Sani a jihar Kaduna', Inji El Rufai

'Na Tsine wa Gwamnatin Uba Sani a jihar Kaduna', Inji El Rufai

  • Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i ya ce zai yi wuya gwamnatin Uba Sani ya yi albarka bayan ya gama tsine mata
  • Ya ce ko a zaɓen ƙananan hukumomin Kaduna da ya gabata, an ga yadda gwamnati ta ƙi sanar da sakamakon zaɓen
  • Nasir El-Rufa'i ya shawarci jama'a a kan yadda za su gudanar da zaɓe, inda ce su karɓi kuɗi ko taliya idan an ba su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana dalilinsa na sukar gwamnatin jihar Kaduna a karkashin Uba Sani.

Ya ce ya san zai yi wuya gwamnatin ta yi adalci a dukkanin zaɓukan da za a gudanar a ƙarƙashin hukumar zabe ta jihar.

Kara karanta wannan

El Rufai: Gwamnatin Kaduna ta karyata zargin ADC ana shirin zaben cike gurbi

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufa'i
Hoton tsohon gwamnan Kaduna lokacin yana gwamna Hoto: El-Rufa’i
Source: Facebook

Nasir El-Rufa’i ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Alheri Rediyo, wadda aka wallafa a shafinsu na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufa’i ya soki gwamnatin Kaduna

A hirar, Nasir El-Rufa’i ya yi alfahari da yadda gwamnatinsa ta tabbatar an gudanar da zabe cikin adalci a lokacinsa.

Ya ce an bai wa sauran jam’iyyu hakkinsu bayan jama’ar Kaduna sun zabe su, inda ya bayyana cewa:

“Fata na a wannan zaben (cike gurbi) shi ne hukumar INEC za ta tsaya ta yi adalci. Amma gwamnatin jihar Kaduna na fidda ran cewa za ta taba yin adalci.”
Gwamnan Kaduna, Uba Sani
Gwamna Uba Sani a yayin wani taro a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Ya kara da cewa kowa shaida ne kan yadda gwamnatinsa ta gudanar da zabukan kananan hukumomi cikin gaskiya da adalci.

A karkashin Sanata Uba Sani, tsohon gwamnan ya bayyana cewa magudi aka yi kuma har yau ba a fitar da sakamakon takarar da aka yi ba.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

Tsohon gwamnan ya ce:.“Har na’urar zabe muka saya don mu tabbatar ba a yi magudi ba. Kuma a lokacinmu, aƙalla kananan hukumomi biyar ko shida ba mu ci zabe ba, duk da mu ne a kan mulki.”
“APC na tsine mata na bar ta da duniya, ita ma gwamnati jihar Kaduna haka.”

Shawarar El-Rufa'i ga matan Kaduna

Tsohon gwamnan ya shawarci masu kada kuri'a, musamman mata a jihar Kaduna da su tabbata sun karɓe duk wani cin hanci da za a ba su a zaɓen da ke tafe.

Ya kara da cewa duk wanda ya ba su taliya, ko kudi, su karba sannan su je su dangwala wa wanda ya fi cancanta.

Tsohon gwamnan, wanda ya nanata cewa APC tsinanniyar jam'iyya ce, saboda haka ya tallata masu jam'iyyar SDP mai alamar doki.

'El-Rufa'i yana cikin APC', Jimoh

A baya, mun wallafa cewa tsohon shugaban hukumar kula da harkokin ruwa ta kasa (NIMASA), Bashir Jamoh, ya ce tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai na nan a APC.

A cewar Jamoh, duk da cewa Nasir El-Rufai ya taba bayyana goyon bayansa ga jam’iyyun SDP da ADC, ba a taba samun wata sanarwa ta ficewarsa daga APC a hukumance ba.

Jamoh ya kwatanta El-Rufai da cibiyar siyasa da ba za a iya cireta daga tarihi ba, yana mai tabbatar da cewa jam’iyyar APC a Kaduna tana tare da shi duk da alakarsa da 'yan adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng

iiq_pixel