"Ƴan Takara 2 ne Za Su Iya Hana Tinubu Cin Zaɓen 2027," Ayodele Ya Gargaɗi Atiku
- Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa ’yan takara biyu daga jam’iyyar ADC na iya hana Shugaba Bola Tinubu lashe zaben 2027
- Rahotanni sun nuna manyan ’yan siyasar adawa da suka rungumi ADC sun haɗa da Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, Peter Obi
- Shugaban cocin IESC ya ce ba iya Shugaba Tinubu ba, har shi kansa Atiku zai iya rasa nasara a zaben saboda 'yan takarar biyu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Lagos – Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin Inri Evangelical Spiritual, ya fitar da wani sabon hasashe game da yadda za ta kaya a zaben 2027.
A babban zaben shugaban kasa mai zuwa, Primate Ayodele ya ce ’yan takara biyu ne za su iya hana Shugaba Bola Tinubu samun tazarce.

Source: Facebook
'Mutane 2 za su hana Tinubu cin zabe'
Legit Hausa ta zakulo wannan sabon hasashen a cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin cocin Inri Evangelical Spiritual na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon Ayodele ya yi hasashen cewa ’yan takarar biyu za su fito ne daga jam’iyyar adawa ta ADC, kuma za su iya hana Atiku Abubakar zama shugaban ƙasa.
Primate Ayodele ya ce:
“Mutane biyu za su iya fitowa takara karkashin jam'iyyar ADC, kuma zau su hana Atiku zama shugaban ƙasa. Za su iya hana Atiku samun tikitin ADC.”
Ya ƙara da cewa:
“Kuma waɗannan mutane biyu, su ne kuma za su iya hana Tinubu sake zama shugaban ƙasa. Da su uku ne, amma yanzu sun rage yawa zuwa mutum biyu.”
Kawancen 'yan adawa a jam'iyyar ADC
Rahotonni sun bayyana cewa tun bayan da ’yan adawa suka rungumi ADC a farkon watan Yuli, ake samun ce-ce-ku-ce kan wannan kawance.
Cikin shugabannin kawancen da ke adawa da Tinubu akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi.
Sauran manyan 'yan siyasa da suka shiga ADC sun hada da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023 Peter Obi; tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai; da tsohon shugaban APC John Oyegun.
Harilayau, akwai tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido; tsohon shugaban PDP na ƙasa Uche Secondus; tsohon gwamnan Neja Babangida Aliyu; tsohon gwamnan Ebonyi Sam Egwu; tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal; da tsohon gwamnan Cross River Liyel Imoke, da sauransu.
A ƙarshen watan Yuli ne, Atiku, wanda ya kasance ɗaya daga cikin wadanda suka kafa PDP, ya fice daga jam’iyyar, inda ake sa ran zai shiga ADC a hukumance.
Ayodele ya gargadi Tinubu kan zaben 2027
Haka kuma, Primate Ayodele ya yi hasashen cewa kafin zaben 2027, matasan Najeriya za su yi zanga-zanga, wadda ka iya shafar damar Tinubu na samun wa’adi na biyu.
Shugaban cocin na IESC ya ce:
“Gwamnatin Tinubu, ba ki magance matsalolin matasa ba. Idan ba a dauki mataki ba, ina hango wata mummunar zanga-zangar matasa.
"Kafin wannan zabe na 2027, matasa za su yi zanga-zanga, kuma hakan zai iya shafar burin gwamnati mai ci na sake lashe zaben shugaban ƙasa.”
Kalli bidiyon a nan kasa:
Ayodele ya hango abin da zai rusa ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya bayyana cewa sai da sihiri ne kawai za a rushe kawancen jam'iyyar ADC.
Ana kallon wannan sabon kawancen na ADC a matsayin babban sauyi a fagen siyasar Najeriya, wanda zai iya zama barazana ga APC a zaɓen 2027
Fitaccen malamin addinin Kiristan ya fadi haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, ciki har da wakilin Legit.ng, a yankin Oke-Afa da ke Legas.
Asali: Legit.ng


