"Ba wanda Ya Isa": Jam'iyyar PDP Ta Nuna Yatsa ga Nyesom Wike

"Ba wanda Ya Isa": Jam'iyyar PDP Ta Nuna Yatsa ga Nyesom Wike

  • Jam'iyyar PDP ta kai makura kan abubuwan da ke faruwa tsakaninta da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike
  • Mai magana da yawun PDP na kasa ya bayyana cewa ba wanda ya isa ya kafawa jam'iyyar hamayyar sharuddan da za ta bi
  • Debo Olugunagba ya nuna cewa bukatar da Wike yake nema kafin a warware rikicin jam'iyyar ba za su amince da ita ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta fito ta nuna yatsa ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Mai magana da yawun PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ce ba wanda ya isa ya sanyawa jam’iyyar sharudda.

PDP ta yi wa Wike martani
PDP ta yi watsi da sharuddan Nyesom Wike Hoto: @OfficialPDPNig, @GovWike
Asali: Facebook

Debo Ologunagba ya yi wannan bayanin ne yayin da yake magana da manema labarai ranar Laraba, 13 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Zan iya soke zaɓen': Jonathan ya faɗi abin da ya kayar da shi a 2015 a hannun Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun na PDP yana mayar da martani ne kan wata magana da ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike, ya yi kwanan nan kan rikicin da ke addabar jam'iyyar.

Wike na takaddama da jam'iyyar PDP

A ranar 22 ga Fabrairun 2025, an sake zabar Dan Orbih, wanda na hannun daman Wike ne, a matsayin shugaban PDP na yankin Kudu maso Kudu a wani babban taro da aka gudanar a Calabar, babban birnin jihar Cross River.

Wike da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, sun halarci taron.

Ministan ya bayyana cewa ba za a sake gudanar da wani babban zabe ba har sai wa’adin shugabannin da aka zaɓa ya kare.

Amma a watan Maris, Umar Damagum, mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, ya yi watsi da taron, yana mai cewa kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar bai amince da zaɓen Dan Orbih ba.

Daga baya jam’iyyar ta kafa kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin Emma Ogidi.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya riga mu gidan gaskiya

A ranar 4 ga Agusta, Wike ya ce rikicin cikin gida na PDP ba zai kare ba har sai jam’iyyar ta amince da babban zaben yankin Kudu maso Kudu.

Jam'iyyar PDP ta yi wa Wike martani

Ologunagba ya ce jam’iyyar ba ta karɓar umarni daga kowa, yana mai cewa kwamitin rikon kwaryar zai ci gaba da aiki har sai an gudanar da sabon zabe a yankin Kudu maso Kudu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

PDP ta yi raga-raga da Nyesom Wike
Mai magana da yawun PDP a wajen wani taro Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter
"A watan Maris na wannan shekarar, wa’adin shugabannin yankin Kudu maso Kudu ya kare bisa ka’ida."
"Jam’iyyar, bisa tsarin da kundinta, ta yanke shawarar kafa kwamitin rikon kwarya na yankin Kudu maso Kudu ta hannun kwamitin gudanarwa na kasa, a karkashin jagorancin Emma Ogidi."
“PDP ba ta karɓar sharadi daga kowa, kuma ba za ta taɓa yi ba. Za mu ci gaba da bin kundin tsarinmu. Muna da kwamitin rikon kwarya na yankin Kudu maso Kudu, kuma suna ci gaba da aiki a matsayin kwamitin rikon kwarya."

Kara karanta wannan

PDP ta sacewa magoya bayan Jonathan da Obi guiwa da aka kafa kwamitin karba karba

"Idan lokacin gudanar da babban taro na cike guraben ya yi, duk mamban da ya cancanta daga wannan yanki zai sami damar tsayawa takara."

- Debo Ologunagba

Sule ya bukaci a kori Wike daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi kira da babbar murya ga jam'iyyar PDP.

Sule Lamido ya bukaci PDP da ta kori Nyesom Wike da sauran wadanda suka yi mata zagon kasa a zaben 2023.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba zai kara halartar tarurrukan PDP ba har sai lokacin da aka kori Wike daga jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel