'Zan Iya Soke Zaɓen': Jonathan Ya Faɗi Abin da Ya Kayar da Shi a 2015 a Hannun Buhari

'Zan Iya Soke Zaɓen': Jonathan Ya Faɗi Abin da Ya Kayar da Shi a 2015 a Hannun Buhari

  • Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ya yi tunanin soke zaben 2015 saboda matsalolin na’urar tantance katin zabe a Kudancin Najeriya
  • Jonathan ya bayyana cewa shi, matarsa da mahaifiyarsa ba su kada kuri’a ba, amma a Arewa an bar mutane su yi zabe ba tare da tantancewa ba
  • Ya ce duk da matsalolin na na'urar 'Card reader', bai dakatar da zaben ba, wanda Muhammadu Buhari na APC ya lashe da rinjayen kuri’u

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya sake magana game da zaben 2015 da ya sha kaye a hannun marigayi, Muhammadu Buhari.

Goodluck Jonathan ya tuna yadda aka gudanar da kada kuri'a a wancan lokaci wanda aka samu bambanci tsakanin Kudu da Arewa.

Kara karanta wannan

Wata 1 da rasuwar Buhari, ma'aikatansa sun yi hawaye, sun fadi kyawawan halayensa

Jonathan ya fadi yadda ya fadi a hannun Buhari a 2015
Jonathan yana gaisawa da Buhari bayan rasa mulki. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Hakan na cikin wani guntun bidiyo yayin yi hira da Jonathan wanda @chude__ ya wallafa a shafinsa na X a yau Alhamis 14 ga watan Agustan 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban na Najeriya ya yi irin wadannan zargi a baya, shekaru bayan barin ofis.

Jonathan ya sha kaye a hannun marigayi Buhari

Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shi ne ya yi nasara a zaben 2015 da aka gudanar.

Buhari daga jam'iyyar APC ya kayar da Shugaban kasa a wancan lokaci, Goodluck Jonathan da ratar kuri'a masu yawa.

Marigayin ya yi mulki har na tsawon shekaru takwas daga 2015 zuwa shekarar 2023 inda Bola Tinubu ya gaji kujerar har zuwa yanzu.

Tun bayan hawan Buhari mulki mafi yawan yan Najeriya ke korafi yayin da kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi da matsin tattalin arziki.

Jonathan ya tuna zaben 2015 da ya kara Buhari
Jonathan ya faɗi kura-kurai da aka samu a zaben 2015. Hoto: Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

Jonathan ya ce akwai kura-kurai a zaben 2015

A cikin bidiyon, Jonathan ya ce da ya so da ya soke zaben duba da abubuwan da suke faruwa yayin kada kuri'a.

Kara karanta wannan

"Ina da tabbaci," Bwala ya hango yadda za ta kaya tsakanin Jonathan da Tinubu a 2027

Jonathan ya ce na'urar katin zaben ta ki tantance shi da matarsa da kuma mahaifiyarsa wanda ya hana su zabe.

Ya ce abin takaici an samu sabanin haka a Arewacin Najeriya wanda aka bar mutane suna yi ba tare da tantacewa ba.

A yayin hirar, Jonathan ya ce:

"A 2015, na’urar katin zabe ta INEC ta ki karɓar katin masu jefa ƙuri’a da dama a Kudancin Najeriya, ni da matata ma mun sha fama.
"Amma a yankin Arewacin Najeriya, an bayar da umarni kowa ya kada kuri’a ba tare da tantancewa ba.
"A lokacin, da na so, zan iya dakatar da zaɓen duk da ana cikin wani irin yanayi, zaben ya yi zafi sosai"

An yi hasashen Jonathan zai zama shugaban ƙasa

A baya, mun kawo muku labarin cewa wani malamin addinin Kirista a Najeriya ya yi hasashen wanda zai dare kujerar shugaban kasa a kasar a shekarar 2027 .

Kara karanta wannan

'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa

Fasto Bomadi Serimoedumu ya yi hasashen tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan zai koma 'Aso Rock' a 2027 idan ya tsaya takara kuma zai yi nasara.

Malamin ya ce a hangensa ya ga Jonathan yana daga tutar PDP sama, zai yi shugabanci shekaru hudu cikin farin ciki da kuma bunkasar tattalin arziki a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.