'Mun Gama Zabi,' APC a Yankin Tinubu Ta Yanke Hukunci kan Zaben Shugaban Kasa

'Mun Gama Zabi,' APC a Yankin Tinubu Ta Yanke Hukunci kan Zaben Shugaban Kasa

  • Shugabannin jam’iyyar APC a Kudu maso Yamma sun bayyana cikakken goyon bayansu ga shugaba Bola Tinubu don yin tazarce a 2027
  • Sun bayyana cewa ba za yi kasa a gwiwa ba wajen kaddamar da shirin fara wayar da kan jama’a tun daga rukunin mazabu gabanin zaben
  • Da yake magana da manema labarai bayan taron, shugaban APC na Kudu maso Yamma, Isaac Kekemeke ya ce sun shirya yi wa Tinubu kamfe

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na Kudu maso Yamma ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kwamitin ya kuma amince Shugaban Kasa ya sake tsayawa takara a babban zaben 2027 da ke tunkaro wa.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
APC a Kudu maso Yamma ta ce Tinubu za ta zaba Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Shugabannin yankin sun kuma bayyana shirin ɗaukar tallata ayyukan Tinubu a kowace mazaba domin sakonya kai ga talaka.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da jita jitar matsala tsakanin Ganduje da Barau Jibrin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagororin APC sun aminta da mulkin Tinubu

Premium Times ta wallafa cewa bayan kammala taronsu a Akure, babban birnin jihar Ondo, a ranar Laraba, shugabannin APC sun ce ba za su bari a bar su a baya wajen tallata Tinubu ba.

Da yake magana da manema labarai bayan taron, shugaban APC na Kudu maso Yamma, Hon. Isaac Kekemeke, ya bayyana cewa:

“Burinmu shi ne Kudu maso Yamma ta yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu abin da Arewa maso Yamma ta yi wa marigayi shugaba Muhammadu Buhari a zabe.”

Kekemeke ya ce kwamitin zartarwa na yankin, wanda ya ƙunshi shugabannin jam’iyya na jihohi shida da 'yan majalisar zartarwa ta ƙasa daga yankin, sun tattauna sosai kan halin da jam’iyyar ke ciki.

APC ta zabura don yi wa Tinubu kamfe

Ya ƙara da cewa, sun kafa kwamiti da zai yi aiki tare da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da sauran gwamnonin yankin domin shirya taro ko gagarumin gangami a ƙarshen watan Satumba.

Kara karanta wannan

Zai koma APC ne? An ga gwamnan adawa ya sanya hula mai tambarin Tinubu a Aso Rock

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
APC a Kudu maso Yamma za ta fara yi wa Tinubu kamfen Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A cewar Kekemeke, ba za su jira lokaci ya kure ba, saboda suna ganin matsayin yankin a matsayin gida ga shugaban kasa ya zama wajibi su jagoranci fafutukar sake zaɓensa.

Shugabannin yankin sun yaba da irin ayyukan da Tinubu ya yi, inda suka ce ya samu yabo daga ƙungiyoyin duniya, cibiyoyin kuɗi na duniya, da kwararrun masana tattalin arziki.

Kekemeke ya bayyana cewa:

“Ana fara ganin sakamakon matakan da ya ɗauka wajen sauya tattalin arzikin ƙasar. Farashin kaya ya fara daidaituwa da raguwa, darajar kuɗin ƙasa ya fara karuwa, ana biyan bashi, kuma martabar Najeriya tana ɗaukaka a idon duniya.”

Bwala: 'Arewa ta aminta da mulkin Tinubu'

A baya, kun ji cewa Hadimin Shugaban Ƙasa na musamman kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa yankin Arewa na gamsuwa ƙwarai da irin salon mulkin Bola Tinubu.

Hadimin Shugaban kuma ƙaryata ikirarin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, da ya ce Arewa na shirin adawa da Tinubu a babban zaɓen 2027.

Babachir Lawal ya zargi gwamnatin Tinubu da watsi da Arewa, yana mai cewa yankin bai samun manyan ayyukan ci gaba da zai bunkasa ta daga gwamnatin tarayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng