Nyesom Wike Ya Sake Samun Yadda Yake So a Tsarin Siyasar Rivers

Nyesom Wike Ya Sake Samun Yadda Yake So a Tsarin Siyasar Rivers

  • Siyasar jihar Rivers na ci gaba da daukar sabon salo bayan an kawo karshen rikicin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike
  • A wannan karon Wike ya shiga cikin jam'iyyun PDP da APC domin nuna karfin da yake da shi a siyasar jihar duk da ya bar kujerar gwamna
  • Ministan na birnin tarayya Abuja ya sake samun iko da tsari, inda ya sanya mutanensa suka zama 'yan takara a zaben kananan hukumomi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ɗauki karin matakai na karfafa ikonsa a tsarin siyasar jihar Rivers.

Hakan ya bayyana ne ta hanyar kaddamar da yakin neman zaɓe na ƙananan hukumomi a jihar.

Wike na ci gaba da yin tasiri a siyasar Rivers
Wike ya kafa yaransa a jam'iyyun APC da PDP Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa an gudanar da taron kaddamar da yakin neman zaɓen jam’iyyar PDP a birnin Port Harcourt a ranar Laraba, 13 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba: Sabuwar rigima ta kunno kai a jam'iyyar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dai shirya gudanar da zaben kananan hukumomin ne a ranar 30 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.

Wike na ci gaba da karfi a siyasar Rivers

A wajen taron, magoya bayan ministan, ciki har da shugaban PDP a jihar, Aeron Chukwuemeke, da kuma Martin Amaewhule, kakakin majalisar dokokin jihar Rivers da aka dakatar, sun yi ta yabon Nyesom Wike.

"Bari na yi amfani da wannan dama na gode wa jagoranmu, Wike, wanda ya sanya wannan kaddamarwa ta yau ta samu nasara."

- Aeron Chukwuemeke

Shi ma Martins Amaewhule, wanda ya kasance tare da sauran ‘yan majalisa 26 masu goyon bayan ministan, ya kwararo yabo ga Wike.

“Muna mika godiya ga jagoranmu na siyasa, ubanmu, Wike, saboda irin jagorancin da ya bai wa PDP da jihar Rivers.”

- Martins Amaewhule

Gwamna Siminalayi Fubara wanda aka dakatar tare da magoya bayansa ba su bayyana a wurin taron ba, sai dai hoton Fubara da aka saka a wani bango a wurin taron.

Kara karanta wannan

'Yan sanda: "Yan siyasa a kano sun yi alkawarin hana zubar da jini a zaben cike gurbi"

Wike na da cikakken iko a tsarin jam’iyyar PDP da ma na jam’iyyar APC a jihar mai arzikin mai.

Shugaban jam’iyyar APC a Rivers, Tony Okocha, abokin siyasar Nyesom Wike ne.

A yayin da ake shirin gudanar da zaɓen a karkashin dokar ta-baci, dukkanin 'yan takara a jam'iyyun APC da PDP, yaran Wike ne.

Hakan ya bayyana cewa Wike ya sake samun cikakken iko a tsarin siyasar jihar Rivers.

Wike na karfafa tasirinsa a siyasar Rivers
Wike ya karbe ikon tsarin siyasar jihar Rivers Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Karanta wasu labaran game da Wike

Jam'iyyar PDP ta amince da bukatun Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin jam'iyyar PDP sun amince da bukatun ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Gwamna Zulum ya mika bukatarsa ga rundunar sojojin sama

Majiyoyi daga jam'iyyar sun bayyana cewa an amince da bukatun ministan ne domin kawo karshen rikicin da ya dade yana addabar PDP.

Nyesom Wike dai ya kafa sharudda ga jam'iyyar PDP wadanda yake so a cika kafin a warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng