"Ta Kare Masa": Bwala Ya Fadi Kuri'un da Tinubu Zai Samu a Yankin Peter Obi
- Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya hango tagomashin da Bola Tinubu zai samu a Kudu maso Gabas
- Daniel Bwala ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai samu kuri'u masu yawa fiye da wadanda ya samu a yankin a shekarar 2023
- Hakazalika, ya ba da tabbacin cewa Peter Obi ba zai hana shi samun kuri'u ba domin tasirinsa ya ragu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana kuri'un da mai girma Bola Tinubu zai samu a yankin Kudu maso Gabas.
Daniel Bwala ya ce yana da tabbacin cewa shugaban kasan zai samu karuwar yawan kuri’u daga yankin Kudu maso Gabas a zaɓen shugaban kasa na shekarar 2027.

Asali: Twitter
Hadimin shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv ranar Laraba, 13 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan
"Bai damu ba": Peter Obi ya ragargaji Tinubu yayin da ya shirya tafiya kasashen waje
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu zai samu kuri'un Kudu maso Gabas
Daniel Bwala ya ce Tinubu na iya samun har zuwa kuri’u miliyan biyu daga yankin, inda ya ce zai ninka sau huɗu ko ma sau shida fiye da abin da ya samu a 2023.
A zaɓen shugaban kasa na 2023, Tinubu ya samu kuri’u 127,370 kacal a yankin Kudu maso Gabas.
"Yadda abin zai kasance shi ne, ban san yadda zan fassara shi ba, amma bari na ɗauki yanki-yanki."
"A Kudu maso Gabas, ina tabbatar muku cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai samu fiye da sau huɗu, idan ba sau shida ba, na kuri’un da ya samu a baya. Zai samu har zuwa miliyan biyu."
- Daniel Bwala
Da aka tambaye shi yadda shugaban kasan zai samu wannan adadi idan Peter Obi na jam’iyyar yana cikin 'yan takara, Bwala ya ce yankin na da yawan masu kada kuri’a, sannan ya yi ikirarin cewa tasirin Obi ya ragu sosai.
Bwala ya yi magana kan Peter Obi
Daniel Bwala ya kara da cewa abin da kawai Peter Obi zai iya samu shi ne shugaban yakin neman zabe a hadakar jam'iyyar ADC.

Asali: Twitter
"Ina gaya muku, ba zai samu tikitin takara a kowace jam’iyya (ADC, PDP, LP) ba. Wannan shi ne Peter Obi. Matsalar yanzu ma ita ce, watakila ma ba zai samu takarar mataimakin shugaban kasa ba idan aka ci gaba da tafiya haka."
"Amma ko Peter Obi ya tsaya takara ko a’a, ya riga ya rasa fiye da kashi 50% na kuri’unsa saboda ba ƙuri’un da aka gina bisa tsari da manufofi bane, an gina su ne bisa magana marar tushe da rarrabuwar kai, kuma idanun ’yan Najeriya sun buɗe.”
- Daniel Bwala
Ya kuma yi nuni da cewa sauya shekar wasu gwamnoni daga Kudu zuwa APC da goyon bayan da gwamnonin jam’iyyun adawa suka bayar, zai kara yawan kuri’un shugaban kasa da farin jikinsa a Kudu maso Gabas kafin zaɓen da ke tafe.

Kara karanta wannan
"Ina da tabbaci," Bwala ya hango yadda za ta kaya tsakanin Jonathan da Tinubu a 2027
Bwala: Tinubu zai kayar da Jonathan
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya yi magana kan zaben 2027.
Daniel Bwala ya cika baki da cewa babu wani dan takara da zai iya hana nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben.
Ya bayyana cewa ko tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya kawo cikas ga tazarcen Shugaba Tinubu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng