"Ina da Tabbaci," Bwala Ya Hango Yadda Za Ta Kaya tsakanin Jonathan da Tinubu a 2027

"Ina da Tabbaci," Bwala Ya Hango Yadda Za Ta Kaya tsakanin Jonathan da Tinubu a 2027

  • Daniel Bwala ya tabbatar da cewa babu wani abu da a zai hana shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tazarce a zaben 2027
  • Hadimin shugaban kasar ya ce a halin da ake ciki yanzu a siyasar Najeriya, babu wani dan siyasa da zai iya buga Tinubu da kasa a zabe
  • Bwala ya ce babu tantama Jonathan ya kara farin jini bayan barin mulki a 2015 amma duk da haka ba zai iya ja da Tinubu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa yana da tabbacin maigidansa, Bola Tinubu zai samu nasara a 2027.

Hadimin shugaban kasar ya ce babu wani dan siyasa a Najeriya da zai iya kifar da shugaba Tinubu a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Bai damu ba": Peter Obi ya ragargaji Tinubu yayin da ya shirya tafiya kasashen waje

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Daniel Bwala ya ba da tabbacin nasarar shugaban kasa, Bola Tinubu a 2027 Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Bwala, ya bayyana haka ne a hirar da aka yi da shi a ciki shirin Politics Today na tashar Channels TV a ranar Laraba, 13 ga watan Agusta, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bwala ya bada tabbacin nasarar Tinubu a 2027

“Na yi nazari kan yanayin siyasar da muke ciki a Najeriya yau, kuma zan yi magana bisa gaskiya ba zato ba.
"Babu wani dan siyasa da ya rage wanda ke da karfin da zai iya kawar da Shugaba Bola Tinubu a kowane fanni,” in ji shi.

Tuni dai manyan ‘yan adawa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, suka kulla hadaka domin kwace mulki daga APC a zaben 2027.

Yan adawa na shirin hada kai da Jonathan

Sauran tawagar hadakar sun hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, da wasu da dama.

Kara karanta wannan

"Ta kare masa": Bwala ya fadi kuri'un da Tinubu zai samu a yankin Peter Obi

Ana kuma ci gaba da kiraye-kirayen neman tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya dawo ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.

Jam'iyyar ADC da PDP na kokarin shawo kan Jonathan duk da cewa har yanzu tsohon shugaban kasar bayyana matsayarsa a fili ba.

Sai dai Bwala ya ce Shugaba Jonathan ya samu karin farin jini a duniya tun bayan barin mulki a 2015.

Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.
Bwala ya zargi wasu yan Arewa da yunkurin yaudarar Jonathan Hoto: Dr. Goodluck Jonathan
Asali: Getty Images

Jonathan zai iya kayar da Tinubu a 2027?

Hadimin shugaban kasar ya kara da cewa Tinubu ya riga ya samu goyon bayan Arewa da Kudu baki daya, don haka Jonathan ba zai iya kayar da shi ba, cewar rahoton Vanguard.

"Wasu tsirarun mutane na kokarin ruɗar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya koma siyasa domin su bata masa suna da yake ginawa tun bayan barin mulki, ta hanyar zama mutum sananne a idon duniya.
"Mutanen da ke zuwa gare shi daga Arewa suna rokon ya tsaya takara, ba su ne suka kore shi ba a baya? Wane tabbaci yake da shi cewa wannan karon suna nufinsa da alheri ne?"

Kara karanta wannan

Ana jita jitar rashin lafiya, Tinubu ya yi magana, ya fadi gwamnonin da zai yi alaƙa da su

- Daniel Bwala.

Bwala ya ce Arewa ta gamsu da Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya yi ikirarin cewa yan Arewa sun gamsu da salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Ya kuma ƙaryata ikirarin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, wanda ya ce Arewa na shirin adawa da Tinubu a zaɓen 2027.

Bwala ya kara da cewa Tinubu na ci gaba da magance matsalolin da suka addabi Arewa kuma mazauna yankin sun shaida haka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262