Sanata Barau Ya Tabo Kujerar Gwamna Abba a Gangamin Zaben Cike Gurbin Kano
- Jam'iyyar adawa a Kano watau APC ta shirya gangamin kamfe yayin da ake shirin zaben cike gurbi a Shanono da Bagwai da karashen na Ghari
- Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya jagoranci jiga-jigan APC zuwa wurin taron da ya mikawa yan takara tuta
- Barau ya ce nasarar APC a wannan zaben cike gurbin zai kara tabbatar da shirinta na kwace kujerar gwamnan jihar Kano a zaben 2027
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Shirye-shiryen zaben cike gurbin dan Majalisar Dokokin Kano mai wakiltar Bagwai da Shanono, ya yi nisa yayin da APC ta shirya gangamin tallata dan takararta.
Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya jagoranci kusoshin APC a gangamin neman goyon bayan al'ummar kananan hukumomin Bagwai da Shanono.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa a ranar Asabar mai zuwa, 16 ga watan Agusta, 2025, hukumar INEC ta shirya zaben cike gurbi a mazabar, tare da karisa zabe a mazabar dan Majalisar jiha na Ghari (Kunchi).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau ya jagoranci manyan APC
Barau ya samu rakiyar Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi Ata, Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar Bichi, da sauran manyan jiga-jigan APC.
Gangamin ya tara dubban jama’a da magoya bayan APC, inda shugabannin jam'iyya suka roki mazauna yankin da su fito kwansu da kwarkwata domin su dangwalawa APC.
A jawabinsa, Sanata Barau Jibrin ya ce zaben dan takarar APC, Ahmad Kadamu, zai ƙara tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta ci gaba da aiwatar da ayyuka a yankin.
Barau ya tabo batun zaben gwamna a 2027
"Ku fito ku kada wa APC kuri'unku a zaben cike gurbi, hakan zai zama farkon nasarorin da za mu samu a zaben gwamna da shugaban kasa mai zuwa a 2027."
Bayan gangamin kamfen, jerin gwanon motocin yakin neman zaben ya wuce zuwa Ghari, inda aka mika tutar jam’iyyar APC ga dan takarar zaben ƙarishe na kujerar.
A nasa jawabin, Injiniya Bichi ya bayyana tabbacin cewa APC za ta lashe kujerun yan majalisar dokokin jiha, yana mai danganta wannan da irin ayyukan da jam’iyyar ta yi a matakin tarayya.

Source: Twitter
Gwamnatin Tinubu za ta yi titi a Shanono/Bagwai
Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a fitar da Naira biliyan 10 domin gina titin Bichi–Bagwai/Shanono–Gwarzo don sauƙaƙa jigilar amfanin gona.
Hon. Abubakar Bichi ya ƙara da cewa aikin yana cikin jerin alkawuran da aka yi wa yankin, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Alaka ta yi tsami tsakanin Ganduje da Barau?
A wani labarin, kun ji cewa alamu sun nuna cewa rikici ya fara raba kan jagororin jam'iyyar APC a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.
Wasu majiyoyi sun yi ikirarin cewa an fara zaman doya da manja tsakanin magoya bayan tsohon shugaban APC na kaaa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Barau Jibrin.
Rahotanni sun nuna cewa APC Kano ta kafa kwamitoci uku don shawo kan ‘ya’yan da suka ji an yi musu rashin adalci domin a daidaita matsalolin cikin gida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

