Tinubu Ya Sakawa Kanwar Abdussamad BUA, Ya ba Ta Mukami a Gwamnatinsa

Tinubu Ya Sakawa Kanwar Abdussamad BUA, Ya ba Ta Mukami a Gwamnatinsa

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Louis Odion da Ummusalma Isiyaka Rabiu a matsayin kwamishinonin FCCPC, inda majalisar dattawa za ta tabbatar da su
  • Odion, daga Edo, tsohon kwamishina ne, kuma tsohon mataimaki na musamman ga Farfesa Yemi Osinbajo a harkokin yada labarai
  • Ummusalma, daga Kano, ta kafa Gidauniyar Usir don tallafawa talakawa, tare da fafutukar kawo ci gaban matasa da mata a siyasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa domin ayyukanta da kawo ci gaba.

Tinubu ya nada Louis Odion a matsayin Kwamishina Mai Kula da Harkokin Gudanarwa, da Ummusalma Isiyaku Rabiu a matsayin Kwamishina (Harkokin ayyuka) na FCCPC.

Tinubu ya ba kanwar BUA mukami a gwamnatinsa
Kanwar Abdussamad mai BUA ta samu mukami a gwamnatin Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Tnubu ya yi sababbin nade-nade a FCCPC

Hakan na cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga a shafinsa na X a daren yau Laraba 13 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, bidiyon Shugaba Tinubu ya bayyana ana tsaka da jita jitar ba shi da lafiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ummusalma, mai shekaru 35 daga jihar Kano, ita ce ta kafa Gidauniyar Usir, ƙungiyar taimako da ke tallafa wa talakawa da al’ummomi.

Ƙungiyarta tana gudanar da shirye-shiryen ilimi, koyon sana’o’i, da ayyukan jin ƙai ga marasa galihu da al’ummomi masu rauni.

Ta na da digiri a fannin Gudanar da Kasuwanci, tare da yin suna wajen kula da al’ummarta a matakin ƙasa.

A matsayinta na yar siyasa mai kishin ƙasa, ta yi fice wajen ƙarfafa shigar matasa da mata a harkokin siyasa da mulki mai inganci.

Tinubu ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa
Tinubu ya ba kanwar Abdussamad Rabiu mukami a gwamnatinsa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Ummusalma Isiyaka Rabiu.
Asali: Facebook

Sakon da Ummusalma ta turawa Tinubu

Yar siyasar ta yi godiya na musamman ga shugaban Tinubu kan wannan babban abin alheri da ya yi mata.

Ummusalma ta wallafa haka a shafinta na Facebook a yau Laraba 13 ga watan Agustan 2025 inda ta dauki wannan mukami a matsayin kalubale domin ta yi aiki tukuru.

Ta ce:

"Mai girma shugaban kasa ina mai tabbatar maka da cewa zan yi duk abin da ya kamata domin sauke nauyin da ka daura mani."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi ruwan mukamai a hukumomin tarayya ana jita jitar ciwo

Ta kuma godewa Seyi Tinubu da Hon. James Abiodun Faleke kan irin gudunmawa da goyon bayansu.

Louis Odion ya zama kwamishina a FCCPC

Har ila yau, Odion, ɗan asalin jihar Edo, gogaggen ɗan jarida ne kuma tsohon Mataimaki na Musamman ga Farfesa Yemi Osinbajo a harkokin yada labarai.

Kafin haka, ya yi aiki a matsayin kwamishinan yada labarai a jihar Edo, inda ya jagoranci manufofin sadarwa da wayar da kai ga jama’a.

Ya kuma yi karatu a jami’ar Buckingham a Birtaniya, da kuma Ilmin shar'a da diflomasiyya daga Jami’ar Legas.

Tinubu ya nada shugabanni a hukumomi

Kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya amince da kafa sababbin kwamitocin lura da aikin hukumar sadarwa ta NCC da asusun USPF.

Idris Olorunnimbe ya zama shugaban majalisar NCC, yayin da Dr. Aminu Maida ya ci gaba a matsayinsa na mai gudanar da aikin hukumar .

Sanarwar ta ce Ministan Sadarwa, Dr. Bosun Tijani, zai jagoranci kwamitin USPF, asusun da ke samar da kudin ayyukan sadawara domin ci gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.