Tsugunne ba Ta Kare ba: Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar PDP

Tsugunne ba Ta Kare ba: Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar PDP

  • Rikicin shugabanci ya sake kunno a jam'iyyar PDP a jihar Imo bayan da aka shigar da kara a kotu
  • Wasu mambobin jam'iyyar sun maka shugaban PDP, hukumar zabe ta INEC kan zaben da aka gudanar a shekarar 2024
  • Daga cikin bukatun da suke nema har da raba shugabannin jam'iyyar daga kan mukamansu saboda ba a yi zabe na gaskiya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Imo - Rigimar shugabanci da ke addabar PDP a Imo ta ƙara tsananta, bayan da mambobi 83, suka kai kara kotu kan shugaban jam’iyyar na jihar, Hon. Austin Nwachukwu.

Fusatattun mambobin na PDP sun hada har da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), da wasu mutane a cikin karar.

An shigar da shugaban PDP kara a gaban kptu
Mambobin PDP sun shigar da shugaban jam'iyya kara gaban kotu Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mambobin sun shigar da karar ne a a gaban babbar kotun tarayya da ke Owerri.

Kara karanta wannan

Ba daraja: Ƴan sanda sun cafke Basarake kan zargin aukawa ƙaramar yarinya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa mambobin PDP suka shigar da kara

Sun dai shigar da karar ne kan yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar na jihar, wanda suka ce cike yake da nuna wariya da kuma take dokoki.

Mambobin na PDP na neman a tsige Austin Nwachukwu da sauran manyan shugabannin jam’iyyar na jihar Imo.

Masu shigar da karar, karkashin jagorancin Lambert Eze, sun zargi jam’iyyar da karya dokar zaɓe ta 2022 da kundin tsarin mulkinta.

Sun ce an hana wasu wakilai da aka zaɓa daga ƙananan hukumomin Ideato ta Arewa da Ideato ta Kudu shiga zaɓen shugabannin jam'iyyar na ranar 31 ga watan Agusta, 2024,

Wannan zaben ne dai ya haifar da Austin Nwachukwu da sauran mambobin kwamitin zartarwar jam'iyyar na jihar.

Mambobin sun nace cewa zaben an yi shi ne ba bisa ka’ida ba, don haka bai da inganci.

Haka kuma, an haɗa da jam’iyyar PDP ta kasa a cikin karar, da wasu mutum 10, ciki har da shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar a ƙananan hukumomin Ideato ta Areqa da Ideato ta Kudu Hon. Chris Ozoemenam da Hon. Dr. Sylvester Durukwuaku.

Kara karanta wannan

'Yan sanda: "Yan siyasa a kano sun yi alkawarin hana zubar da jini a zaben cike gurbi"

Mambobin PDP sun je kotu a Imo
Mambobin PDP sun kai shugaban jam'iyya kara a kotu Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wadanne bukatu suka nema?

Masu shigar karar na rokon kotu da ta soke sakamakon zaben, ta hana shugabannin da ke kan mulki yanzu ci gaba da kiran kansu shugabannin jam'iyyar.

Sun kuma bukaci kotun ta bayar da umarnin gudanar da sabon zaɓen shugabanni wanda zai haɗa dukkan wakilan da suka cancanta su yi zabe.

Masu karar mai lamba FHC/OW/CS/51/2025 sun shigar da ita ne ta hannun lauyansu, K.U. Alisigwe.

PDP ta amince da bukatun Nyesom Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta amince da bukatun ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, don samun zaman lafiya a cikinta.

Majiyoyi sun bayyana cewa PDP ta amince da dukkanin bukatun da ministan ya nemi kafin ya bari a warware rikicin da ya addabi jam'iyyar.

Sun bayyana cewa jam'iyyar PDP ta amince da.bukatun ne domin kawo karshen adawar da Wike yake yi mata ta hanyar hana ta sakat.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng