'Za Mu More': An Faɗi Dalilai da Ke Nuna Jonathan ne Mafi Dacewa da Bukatun Arewa

'Za Mu More': An Faɗi Dalilai da Ke Nuna Jonathan ne Mafi Dacewa da Bukatun Arewa

  • Wani jigon PDP ya bayyana amfanin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan zai yi wa Najeriya idan ya koma mulki
  • Umar Sani, ya ce tsohon shugaban kasa, Jonathan na da dabarar farfado da tattalin arzikin Najeriya idan ya samu nasara
  • Sani ya bayyana cewa Jonathan ba zai yi fiye da wa’adi daya ba, saboda doka ta hana hakan, kuma hakan zai amfanar da Arewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wani jigon jam’iyyar PDP ya yi magana kan takarar shugaban kasa a zaben 2027 da za a gudanar a Najeriya.

Umar Sani, ya ce tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na da dabarar farfado da tattalin arzikin Najeriya.

An fadi ci gaban da Jonathan zai kawo wa Arewa
Jigon PDP ya ce Jonathan ne mafi dacewa da takara a 2027. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Facebook

Sani ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin amsa tambayoyi a shirin ‘The Morning Brief’ na gidan talabijin na Channels da ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

'Na gano shi a 'Aso Rock': Malami ya faɗi wanda zai zama sabon shugaban ƙasa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP na zawarcin Jonathan kan zaben 2027

Wannan martani na zuwa ne yayin da ake ta hasashen Jonathan zai iya sake fitowa takara a zaɓen 2027 da ke tafe

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa jam'iyyar PDP tana zawarcin tsohon shugaban kasar wanda ya yi mulki a karkashinta.

Mataimakin sakataren jam'iyyar, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da cewa wasu daga cikin jiga-jigan PDP har da gwamnoni suna kokarin shawo kan Jonathan kan lamarin.

An yi hasashen ADC na tattaunawa da Jonathan

Har ila yau, wasu rahotanni sun kara da cewa jam'iyyar haɗaka ta ADC tana tattaunawa da Jonathan domin ya fito mata takara a 2027.

An ce hakan na neman kawo cikas ga takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda ya bar PDP zuwa ADC.

Sai dai hadimin tsohon dan takarar a PDP, Paul Ibe ya ce Atiku dan siyasa ne kuma bai tsoron kowa a 2027.

Kara karanta wannan

2027: Komai na iya faruwa da takarar Atiku da ake hasashen Jonathan zai dawo ADC

Jigon PDP ya yi magana kan takarar Jonathan a 2027
Dan PDP ya ce Arewa za su son Jonathan kan Peter Obi. Hoto: Goodluck Jonathan, Peter Obi.
Source: Facebook

Jigon PDP ya magantu kan takarar Jonathan

Yayin da ake shirin zaben 2027, jigon PDP, Sani ya ce zabin da yafi dacewa ga PDP shi ne Jonathan, wanda ya ce yafi dacewa ga yankin Arewa.

Ya ce Jonathan ba zai yi wa'adi fiye da daya ba saboda ya kasance tsohon shugaban kasa da ya mulki a baya, cewar Daily Post.

Ya ce:

“Saboda haka ba mu duba Jonathan daga ɓangaren yarjejeniya ba. An riga an warware hakan.
"Doka ta riga ta magance batun nan a matsayinsa na tsohon shugaban kasa.
“Ba zai iya yin fiye da wa’adi daya ba, domin doka da kundin tsarin mulki suka hana hakan, zai yi wa’adi daya ya tafi."

Sani ya bayyana cewa yankin Arewa zai fi son Jonathan ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar maimakon Peter Obi a 2027.

Fasto ya ce Jonathan zai zama shugaban ƙasa

Kara karanta wannan

An yi rashi a Najeriya, babban Sarki ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 82

A baya, mun ba ku labarin cewa Malamin addinin Kirista a Najeriya ya yi hasashen wanda zai dare kujerar shugaban kasa a shekarar 2027.

Fasto Bomadi Serimoedumu ya yi hasashen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai koma 'Aso Rock' a 2027 idan ya tsaya takara.

Malamin ya ce a hangensa ya ga Jonathan yana daga tutar PDP sama, zai yi shugabanci shekaru hudu cikin farin ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.