Zai Koma APC ne? An ga Gwamnan Adawa Ya Sanya Hula Mai Tambarin Tinubu a Aso Rock

Zai Koma APC ne? An ga Gwamnan Adawa Ya Sanya Hula Mai Tambarin Tinubu a Aso Rock

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da Gwamna Soludo na jihar Anambra yau Talata a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • An ga Gwamna Charles Soludo sanye da hula mai tambarin Bola Tinubu a lokacin da ya isa Aso Rock duk da kasancewarsa dan jam'iyya APGA
  • Bayan ganawa da shugaba Tinubu, Farfesa Soludo ya bayyana cewa shugaban kasa abokinsa ne da suka shafe sama da shekaru 20 suna tare

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaba Bola Tinubu a ranar Talata ya karɓi bakuncin Gwamna Charles Chukwuma Soludo na Anambra a fadar gwamnati da ke Abuja.

Yayin wannan ziyara, Gwamna Soludo ya sa labule da Shugaban Kasa, Bola Tinubu, inda suka tattauna kan batutuwan da har yanzu ba a bayyana ba.

Kara karanta wannan

Me ake kullawa: Na hannun daman Kwankwaso ya sake ganawa da Shugaba Tinubu

Shugaba Tinubu tare da Gwamna Soludo.
Gwamna ya sanya hula da tambarin Tinubu a ziyarar da ya kai fadar shugaban kasa Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Soludo ya sanya hula da tambarin Tinubu

The Cable ta ruwaito cewa lokacin da gwamnan ya isa fadar shugaban kasa, an ga tambarin Bola Tinubu a jikin hular da ya sanya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Soludo dai shi ne gwamnan Anambra tun watan Maris 2022, bayan ya gaji taohon gwamna, Willie Obiano.

Kafin ya shiga siyasa, Farfesa Soludo ya yi aiki a matsayin gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) daga 2004 zuwa 2009.

Ko da yake Soludo ɗan jam’iyyar adawa ta APGA ne, kwanakin baya ya fito ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Soludo yana neman wa’adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar Anambra da za a yi a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Ana ganin watakila wannan ganawa da Shugaba Tinubu ya yi da gwamnan tana da nasaba da zaben gwamnan Anambra mai zuwa.

Gwamna Soludo ya ce Tinubu abokinsa ne

Kara karanta wannan

Abubuwa 8 da suka bambanta Shugaba Tinubu da su Buhari, Jonathan da 'Yar Adua

Da yake zantawa da masu dauko rahoto a fadar shugaban kasa bayan ganawa da Tinubu, Gwamna Soludo ya ce ya jima yana tare da shugaban kasa.

A cewarsa, abokantakarsa da shugaba Bola Tinubu ta kai shekara 22 kuma ba za ta karye saboda bambancin siyasa ba, rahoton Channels tv.

Gwamnan Anambra ya bayyana tattaunawar da suka yi a matsayin “mai daɗi ƙwarai,” sannan ya ce shugaban ƙasa na cikin “ƙoshin lafiya da nishadi.”

Gwamna Soludo na jihar Anambra.
Gwamna Soludo ya jaddada goyon bayansa ga Shugaba Tinubu Hoto: Charles Chikwuma Soludo
Source: Facebook

Soludo ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu

Ya ƙara da cewa:

"Shugaba Tinubu abokina ne. Mun shafe shekaru 22 muna tare, don haka ba za ka ƙi abokinka na tsawon lokaci ba.
"Ina goyon bayansa, kuma na ji dadin kwararan matakan da ya dauka, musamman a fannoni na tattalin arziki da sauye-sauye. Muna kan hanya madaidaiciya, kuma dole mu ci gaba.”

Tinubu ya yi nadi kuma ya soke a hukumar FCC

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauke Muheeba Dankaka daga matsayin shugabar hukumar FCC awanni bayan nadin ta.

Wannan naɗi da sokewa mai ban mamaki ya haifar da ruɗani a ƙasar, inda wasu manyan mutane, ciki har da Sarkin Ilorin, suka taya Muheeba Dankaka murna.

Awanni hudu bayan sabunta nadin Muheeba, Bola Tinubu ya tunbuke ta sannan ya maye gurbin da tsohuwar yar Majalisa, Ayo Hulayat Omidiran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel