Ana Jita Jitar Rashin Lafiyar Tinubu, Sanata Ya Fadi Halin da Shugaban Kasa Ke Ciki
- Orji Uzor Kalu ya yi karin haske kan rashin lafiyar shugaban kasa, Bola Tinubu da ake ta yadawa a Najeriya
- Sanatan da ya fito daga jihar Abia ya karyata jita-jitar cewa Tinubu yana cikin mummunan yanayi na rashin lafiya
- Ya ce ya yi magana da Tinubu ta waya kuma yana shirin tafiya Japan da Brazil domin wani taro mai muhimmanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Sanata Orji Uzor Kalu ya warware jita-jitar da ake yadawa kan cewa Bola Tinubu yana fama da rashin lafiya.
Sanata Kalu, wanda ke wakiltar mazabar Abia Arewa a majalisar dattawa, ya musanta labarin da ake yadawa kan shugaban.

Source: Twitter
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Sanatan ya wallafa a daren jiya Litinin 11 ga watan Agustan 2025 da muke ciki a Facebook.

Kara karanta wannan
'Mun yi Allah wadai': Atiku ya fadi 'gaskiyar' abin da ya sa EFCC ta tsare Tambuwal
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi ta yada cewa Tinubu bai da lafiya
Majiyoyi sun bayyana cewa ana ta yada zancen cewa shugaban kasa yana cikin wani hali na rashin lafiya mai tsanani.
Wannan bayani da ake yadawa a Najeriya ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta da martani daga yan kasar.
Wasu na kiran hukumomi da su fito su fadawa al'umma gaskiya kan halin da shugaban ke ciki.
Wane martani fadar shugaban kasa ta yi?
Daga bisani, fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa kan lamarin inda ta ke karyata rahoton da ake yadawa.
Fadar shugaban kasa ta musanta wannan jita-jitar, inda ta bayyana cewa shugaban kasa yana gudanar da ayyukansa daga gida ba tare da wata matsala ba.

Source: Facebook
Sanata Kalu ya magantu game da lafiyar Tinubu
A cikin wani bidiyo, Sanata Kalu ya ce ya yi magana da shugaban kasa a wayar salula a ‘yan sa’o’in biyu da suka wuce a daren jiya Litinin 11 ga watan Agustan 2025.
Sanata Kalu ya tabbatar da cewa Tinubu yana cikin koshin lafiya, sai dai ya ce kowa ka iya jin kasala ko rashin jin daɗin fita waje wani lokaci.
Ya ce:
“Na yi magana da shi awa biyu da suka wuce, yana cikin koshin lafiya kuma yana shirin tafiya Japan tare da tsayawa a Brazil.
“Kowa yana iya jin kasala, kamar kwana uku da suka wuce, na shaida wa ‘yata cewa zan huta a sama, na zauna can.”
Ya bayyana cewa babu laifi idan shugaban kasa bai ji daɗin fita ba, kuma hakan bai nuna cewa yana cikin wani hali mai tsanani.
Sanatan ya roki ‘yan siyasa su daina yada jita-jita kan lafiyar shugaban kasa, yana mai jaddada bukatar hada kai wajen farfado da tattalin arzikin kasa.
Babachir Lawal ya sake sukar gwamnatin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya yi kakkausar suka kan salon mulkin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Babachir Lawal ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana nuna son kai tare da fifita 'yan kabilarsa a gwamnatinsa.
Ya nuna cewa da ace ya samu mukami a gwamnatin Tinubu, da tuni ya yi murabus don ba zai iya aiki da shugaban ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
