Me Ake Kullawa: Na Hannun Daman Kwankwaso Ya Sake Ganawa da Shugaba Tinubu
- Na hannun daman madugun tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanya labule da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Honarabul Abdulmumin Jibrin ya gana da shugaban kasan ne a fadarsa ta Aso Rock Villa da ke babban birnin tarayya Abuja
- Ganawar Abdulmumin Jibrin da Shugaba Tinubu dai na zuwa ne, bayan sun yi irin ta a makonni biyu da suka gabata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Na kusa da madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Abdulmumin Jibrin, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Abdulmumin Jibrin ya gana da mai girma Bola Tinubu ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Abdulmumin Jibrin ya gana da Shugaba Tinubu ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdulmumin Kofa ya sake ganawa da Tinubu

Kara karanta wannan
Shugabar FCC tana murnar Tinubu ya tsawaita wa'adinta, an sanar da korar ta daga ofis
Ganawar su dai ta kasance karo na biyu da suka hadu cikin makonni biyu a lokacin da ake ganin za a samu wasu sauyi a siyasar Najeriya ma
Zaman da aka yi a ranar Lahadi tsakanin shugaban ƙasa da ɗan majalisar wakilan ta ɗauki tsawon sa’o’i biyu, daga ƙarfe 9:00 na dare zuwa 11:00 na dare.
Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa ganawar na iya zama mai alaka da dangantaka tsakanin Tinubu da Kwankwaso, da kuma ƙara yawaitar ra’ayoyin adawa da jam’iyyar APC a wasu sassan Arewacin Najeriya.
Sai dai Abdulmumin Jibrin ya ƙi yin bayani kan manufar taron lokacin da manema labarai na fadar shugaban ƙasa suka tambaye shi.
Ganawar dai na iya taɓo batun dangantaka tsakanin tsohon gwamnan Kano da Shugaba Tinubu, da kuma ƙara karuwar ra’ayin adawa da APC a wasu sassan Arewa.

Source: Twitter
A ranar 30 ga watan Yulin 2025, Abdulmumin Jibrin ya hadu da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa.
Ya shaida wa ‘yan jarida bayan ganawa da Tinubu tattaunawar ta su ta fi karkata ne kan haɗin kan ƙasa da cigaba.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban ƙasa ta dura kan Obasanjo, ta yi masa gori bayan shekaru 8 a mulki
Da aka tambaye shi ko ganawar tana da alaƙa da shirin komawa jam’iyyar APC, Jibrin bai bada amsa kai tsaye ba, sai dai ya ce “komai na iya faruwa”.
Abdulmumin Jibrin dai na da kyakkyawar alaka tsakaninsa da Tinubu da kuma Kwankwaso.
Karanta wasu labaran kan Kwankwaso
- Bayan saɓani ya shiga tsakani, Shugaba Tinubu ya gana da na hannun daman Kwankwaso
- Sunan Kwankwaso ya fito: Malami ya samu wahayin wanda zai yi wa Madugu mataimaki
- Fadar shugaban kasa ta sake magana kan 'haduwar' Tinubu da Kwankwaso
- "Ku ankara": NNPP ta yi kira da babbar murya ga matasan Arewa kan Kwankwaso
Shugaban NNPP: Kwankwaso na iya komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban tsagin jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Jibrin Doguwa, ya yi magana kan yiwuwar komawar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa APC.
Jibrin Doguwa ya bayyana cewa akwai yiwuwar jagoran na Kwankwasiyya ya koma jam'iyyar APC don yin aiki tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban na NNPP ya nuna cewa ba abin mamaki ba ne idan Kwankwaso ya koma APC, domin dama siyasa ta gaji haka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng