Ministan Buhari Ya Karyata Amaechi kan Batun Hada Kai da 'Yan Adawa a Kawo ADC
- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya musanta zargin cewa da shi aka kafa sabuwar kawancen ADC da ke adawa da Bola Tinubu
- Dr. Kayoe Fayemi ya bayyana cewa har yanzu yana tare da APC, kuma babu kamshin gaskiya a ikirarin cewa su ne suka farfado da ADC
- Wannan na zuwa a matsayin martani ga wasu kalamai da aka alakanta da tsohon gwamnan jihar Ribas watau Rotimi Amaechi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ekiti – Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya karyata zargin cewa da shi ne ya kafa sabuwar kawancen jam’iyyar ADC tare da tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi.
A baya-bayan nan, wasu rahotanni sun ambaci wata sanarwa da ake alakanta da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi da ke cewa tare suka jagoranci kafa kawancen kafin bude kofarta ga wasu ‘yan siyasa.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Fayemi ya yi wannan karin haske ne a ranar Lahadi ta hannun ofishin yada labaransa a Abuja, wanda Ahmad Sajoh ya sanya wa hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fayemi ya karyata hannunsa a hadakar ADC
Vanguard ta wallafa cewa Sajoh ya ce an gudanar da bincike sosai amma ba a samu wani kwakkwaran shaida ba ko kuma kafar yada labarai mai inganci da ta alakanta Amaechi da kalaman ba.
Ya yi zargin an kirkiri maganganun ne da gangan, tare da gargadi kan yadda ake yawan danganta karya ga fitattun mutane don cutar da wasu ko neman mabiya.

Source: Facebook
Ya jaddada cewa Fayemi na nan daram a matsayin dan jam’iyyar APC mai mulki kuma daya daga cikin jagororinta a jihar Ekiti.
A cewarsa:
“Muna sanar da cewa wannan ikirari ba shi da tushe. Fayemi na nan daram a matsayin jigo kuma dan jam’iyyar APC a jihar Ekiti.”
Sajoh ya kara da cewa tsohon gwamnan ya sha bayyana a bainar jama’a cewa yana da cikakkiyar biyayya ga APC, har ma yana goyon bayan gwamnan jihar, Biodun Oyebanji, domin ya sake tsayawa takara a jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Tsohon gwamnan Legas zai bar tafiyar Tinubu ya koma ADC? Ambode ya fayyace gaskiya
Ana rade-radin Fayemi ya bar APC
An dade ana yada jita jita a kan siyasar Fayemi, musamman saboda ba ya fitowa sosai a harkokin siyasa tun bayan kammala wa’adinsa a watan Oktoba 2022.
Sai dai Sajoh ya ce duk da hakan, har yanzu Fayemi yana aiki da jam’iyyar APC a jihar Ekiti kuma yana halartar tarurrukan jagororin jam’iyyar a jihar.
A cikin watannin baya-bayan nan, jam’iyyar ADC wadda ke daga cikin kananan jam’iyyun adawa ta fara jan hankalin wasu fitattun ‘yan siyasa da ke adawa da APC.
Fayemi ya magantu kan ficewa daga APC
A wani labarin, mun wallafa cewa Tsohon Gwamnan Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, ya karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya fice daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasa.
A kwanakin baya, wasu rahotanni sun yi ta yadawa cewa Fayemi na cikin jerin manyan ‘yan siyasa da ke shirin barin APC saboda sabani da ake zargin ya taso a cikin jam’iyyar.
A wata sanarwa da tsohon gwamnan ya fitar a ranar Litinin, 10 ga watan Maris, 2025, ya bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne, kuma har yanzu yana tare da APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
