2027: 'Dan Majalisa Ya Yi Hasashe kan Yiwuwar Takara tsakanin Tinubu da Jonathan

2027: 'Dan Majalisa Ya Yi Hasashe kan Yiwuwar Takara tsakanin Tinubu da Jonathan

  • Ana ci gaba da hasashen cewa Goodluck Jonathan na iya yin takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027
  • 'Dan majalisar wakilai daga jihar Kogi, Leke Abejide, ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zabe cikin sauki idan ya yi takara da Jonathan
  • Leke Abejide ya bayyana cewa mafi yawan jihohin kasar nan za su kada kuri'unsu ne ga Shugaba Tinubu don ya yi tazarce

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yagba ta Gabas/Yagba ta Yamma/Mopamuro a jihar Kogi, Leke Abejide, ya yi magana kan yiwuwar fafatawa tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Goodluck Jonathan a zaben 2027.

Leke Abejide ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2027 da babban rinjaye idan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yanke shawarar tsayawa takara.

Kara karanta wannan

'Na gano shi a 'Aso Rock': Malami ya faɗi wanda zai zama sabon shugaban ƙasa a 2027

Dan majalisa ya hango nasarar Tinubu kan Jonathan
Dan majalisa ya ce Tinubu zai kayar da Jonathan a 2027 Hoto: @GEJonathan, @DOlusegun
Asali: Getty Images

Leke Abejide, wanda babban jigo ne a jam’iyyar ADC, ya yi wannan furuci ne a lokacin wata hira da aka yi da shi a shirin Mic On podcast da aka sanya a shafin X, a ranar Lahadi, 10 ga watan Agustan 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin 'yan kwanakin nan ana ta rade-radin yiwuwar dawowar Jonathan cikin fafutukar neman kujerar shugaban kasa a zaben 2027.

''Dan majalisar ya hango nasarar Tinubu kan Jonathan

Sai dai, Leke Abejide na ganin cewa takarar Jonathan ba za ta yi wa Tinubu illa ba, sai dai ta kara karfafa damarsa ta yin tazarce a zaben shugaban kasa na 2027.

A cewar Leke Abejide, Tinubu zai iya samun nasara a jihohi sama da 32, inda zai iya faduwa kawai a jihohin Anambra da Abia.

"Addu’ata ita ce su yi takara a haka (daga jam'iyyu daban-daban), kuma Asiwaju zai ci jihohi 32. Watakila ya fadi a Anambra da Abia, amma zai ci Ebonyi, har ma zai iya lashe fiye da jihohi 32."

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Legas zai bar tafiyar Tinubu ya koma ADC? Ambode ya fayyace gaskiya

- Leke Abejide

Meyasa Tinubu zai ci zabe a 2027?

'Dan majalisar ya danganta farin jinin Tinubu da irin kokarin gwamnatinsa wajen inganta hanyoyin sufuri da tsaro a kasar.

Ya bayyana cewa ya yi tafiya a wasu sassan Arewacin Najeriya a baya-bayan nan, kuma ya ganewa idonsa yadda tsaro ya inganta.

Leke Abejide ya hango nasarar Tinubu
Leke Abejide na ganin Tinubu zai yi nasara a zaben 2027 Hoto: Leke Abejide
Asali: Twitter
"Na fito daga Kano kwanan nan, ina Kano a ranar Laraba kuma na kwana a can. Na zo Kaduna a mota safiyar Asabar. Babu matsalar tsaro, hanya tana da kyau, sannan na hau jirgin kasa zuwa Abuja safiyar Lahadi kuma zan iya tabbatar maka cewa mutane suna cikin farin ciki."

- Leke Abejide

An bukaci a goyawa Tinubu baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban kusa a jam'iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya mika kokon bararsa ga 'yan Arewa.

Oyintiloye ya roki manyan 'yan siyasar Arewa da su goyi bayan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Jigon na jam'iyyar APC ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya gudanar da ayyukan da suka kamata su sanya ya kara kwashe wasu shekara hudu a kan mulkin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel