Rikicin cikin Gida: PDP Ta Amince da Bukatun Wike, an Gano Dalili

Rikicin cikin Gida: PDP Ta Amince da Bukatun Wike, an Gano Dalili

  • Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike ya dauki lokaci yana takum saka da jam'iyyarsa ta PDP mai adawa a Najeriya
  • Domin warware rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP, ta amince da bukatun da Nyesom Wike ya gabatar
  • Wannan mataki dai na da fatan ganin an cewa an kawo karshen rikicin jam'iyyar yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta amince da muhimman bukatun tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan babban birnin tarayya Abuja na yanzu, Nyesom Wike.

Jam'iyyar PDP ta amince da bukatun ne domin rage rikice-rikicen cikin gida da kuma farfadowa kafin zaben 2027,

PDP ta yarda da bukatun Wike
PDP ta amince da bukatun Nyesom Wike Hoto: @GovWike, @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce wasu majiyoyi na cikin gida a jam’iyyar PDP ne suka tabbatar mata da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyin sun ce wannan matakin wani ɓangare ne na dabarar haɗa kan jam’iyyar da kuma magance matsalolin da suka dade suna faruwa a cikinta.

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya yi hangen nesa, ya gano hanyar kwace mulki a hannun APC

Wike ya gabatar da bukatunsa ga PDP

Wike, wanda ke da babban tasiri a PDP, ya dage a kan a ware tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ga yankin Kudu.

Sannan yana so a bar Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa, tare da amincewa da zaben shugabannin jam'iyyar a yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

Meyasa PDP ta amince da bukatun Wike?

A cewar wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar, yanzu an amince da waɗannan bukatun, wanda a cewarsu hakan ya cire duk wata hujja da Wike zai yi amfani da ita wajen ci gaba da adawa da tafiyar jam’iyyar.

"Jam’iyyar ta zauna ta amince da komai da Wike yake so. Yana so Anyanwu ya zama sakataren jam’iyyar, kuma hakan ya samu. Yana so shugabannin jam’iyyar su bayyana cewa tikitin shugaban ƙasa za a ba Kudu, kuma an amince."
"To yanzu, a wane dalili ne Wike zai ci gaba da adawa da jam’iyyar? Babu dalili."

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya samo mafita ga PDP kan mutanen da suka yi mata zagon kasa a 2023

- Wani shugaba a PDP

Masu lura da harkokin cikin jam’iyyar na ganin wannan mataki na rarrashin Wike a matsayin dabarar hana karin sauya sheka daga PDP da kuma ƙara samun goyon baya a Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, inda yake da tasiri mai ƙarfi.

Ana ganin wannan mataki na da muhimmanci kafin babban taron PDP da za a gudanar a watan Nuwamba, wanda a lokacin za a kammala batun rabon mukamai da shugabanci.

Wike ya gabatar da bukatunsa ga PDP
PDP ta yarda da bukatun Nyesom Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Jam'iyyar PDP na jiran Goodluck Jonathan

A halin yanzu, PDP tana sa ido sosai kan yiwuwar dawowar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan cikin siyasa, wanda jinkirin bayyana manufarsa ta tsayawa takara a 2027 ya sa jam’iyyar ta kasance cikin ruɗani.

Wasu na ganin cewa tsayawar Jonathan na iya sauya tsarin siyasar ƙasar nan, musamman idan aka haɗa shi da abokin takara irin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Sule ya bukaci a kori Wike daga PDP

Kara karanta wannan

Wike ya kai PDP makura, an sanya lokacin hukunta ministan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ba jam'iyyar PDP shawara.

Sule Lamido ya bukaci PDP ta kori Nyesom Wike tare da sauran wadanda suka yi mata zagon kasa a lokacin zaben 2023.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba zai ci gaba da halartar tarurrukan jam'iyyar ba har sai an kori wadannan mutanen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel