ADC: Amaechi Ya Kada Hantar Tinubu kan Zaben 2027, Ya Fadi Illar da Zai Yi Masa
- Tsohon minista, Rotimi Amaechi ya ce zai doke Bola Tinubu a 2027 idan ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC
- Ya zargi gwamnoni da hukumomin gwamnati da amfani da kudin jama’a wajen magudin zabe, ya ce shi ba ya shiga irin wannan
- Amaechi ya amince Peter Obi ya ci zabe a Rivers 2023, ya yi alkawarin kare gaskiya da bin tsarin karba-karba idan ya samu mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, ya bude aiki kan zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Amaechi ya ce zai iya doke Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 idan ya samu tikitin jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya.

Source: Twitter
Yadda Amaechi ke gudun shiga magudin zabe
Amaechi ya bayyana haka ne a hirar X Spaces, da TheCable ta bibiya inda ya kara da cewa bai taba shiga magudin zabe ba.

Kara karanta wannan
"Idan ban yi ba zan yi murabus": Amaechi ya fadi abin da zai yi idan ya kayar da Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan Rivers ya kuma ce yana gujewa shiga kwamitin shirya zabe na APC saboda gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.
Ya ce bai taba fafatawa da Tinubu a zabe ba, amma yana sane da karfi da kuma rauninsa, ya yi ikirarin zai iya doke shi a ADC.
Amaechi ya kalubalanci kowanne dan siyasa ya kawo hujja cewa ya taba shiga magudi, ya ce ya ki shiga duk wani kwamitin zabe da APC ta ba shi.
Ya zargi cewa yawanci magudin zabe, gwamnoni suna da hannu, tare da karkatar da kudaden jama’a daga hukumomin gwamnati domin amfanin zabe.

Source: Facebook
2023: Amaechi ya fadi wanda ya ci zaben Rivers
Amaechi ya ce zai fada wasu abubuwa ne idan ya samu nasarar lashe zaben fitar da gwani na ADC, ya yi alkawarin hana magudin zabe gaba daya.
Ya kara da cewa zai yi afuwa ne kawai idan an gabatar da hujja mai karfi cewa ya taba shiga cikin magudi a wani zabe, cewar Tribune.
Amaechi ya amince da cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ci zabe a jihar Rivers a 2023, kodayake sakamakon ya bambanta.
Bukatar Amaechi a baya kan wa'adin mulki
A baya, a ranar 3 ga Yuli, Amaechi ya ce zai yi wa’adin shekara hudu kacal idan ya samu tikitin ADC domin tabbatar da tsarin karba-karba.
Amaechi ya ce a halin yanzu Najeriya na bukatar kiyaye yarjejeniya wacce ta ke bai wa Kudu da Arewa wa’adin shekaru takwas-takwas a mulki.
Ya koka kan shugabancin Tinubu duba da tsare-tsaren da yake dauka da suke jikkata jama'a a Najeriya.
Dan APC ya magantu kan ADC, Amaechi
Dan a mutun APC a Gombe, Muhammad Ibrahim Bk ya ce Amaechi yana bata lokacinsa ne kawai.
Ya ce:
"Idan Amaechi na zagin APC ina tsammanin su suka kafa ta kuma ya yi shekaru yana minista."
Bk ya ce abin takaici ne a yanzu da zarar mutum ya rasa mulki sai ya fara zage-zage.
Atiku ya fadi manufar kafa ADC
Mun ba ku labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tabo batun manufar kafa hadakar 'yan adawa karkashin ADC.

Kara karanta wannan
Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5
Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba an kafa hadakar ba ne don cika muradun kashin kai na jagororinta ba.
Tsohon dan takarar shugaban kasan ya nuna manufar kafa hadaka ita ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta a karkashin mulkin APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
