Sule Lamido Ya Samo Mafita ga PDP kan Mutanen da Suka Yi Mata Zagon Kasa a 2023
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu shafaffu da mai ke yin abin da suka ga dama a PDP
- Alhaji Sule Lamido ya yi kira da a hanzarta hukunta mutanen da suka yi fito na fito da jam'iyyar adawar lokacin zaben shekarar 2023
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa zai kauracewa tarurrukan kwamitin amintattun PDP har sai an ladabtar da irin wadannan mutanen
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi kira da a gaggauta korar ministan Abuja, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom; da kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu,
Sule Lamido ya bukaci a kori mutanen ne bisa zargin aikata ayyukan da suka ci karo da manufar jam’iyyar PDP a lokacin babban zaɓen 2023.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv a ranar Juma’a, 8 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanne mutane Sule Lamido yake so a kora?
Sule Lamido ya ce dole ne PDP ta nuna jagoranci ta hanyar hukunta mambobin da suka fito fili suka yi aiki don adawa da manufar jam’iyyar.
"Dukkan waɗanda suka karya dokar jam’iyya, su Wike, su Ortom, su Ikpeazu da sauran su, waɗanda suka fito fili suka yi yaƙin neman zaɓen adawa da PDP a zaɓen 2023, sannan kuma suke cewa za su yi wa APC aiki a 2027, ya kamata a kore su daga jam’iyyar."
Sule Lamido ya koka da halin PDP
Sule Lamido ya nuna takaicinsa kan abin da ya kira da al’adar yin abin da kowa ya ga dama ba tare da hukunci ba a cikin PDP, yana mai cewa hakan ya daɗe yana faruwa ba tare da an ɗauki mataki ba.

Kara karanta wannan
Sule Lamido ya raba gardama a PDP, ya hasko wanda zai iya ba da mamaki a zaɓen 2027
"Tun bayan kammala zaɓen fitar da gwanin 2022 wanda ya kai ga zaɓen 2023, akwai wasu mutane da saboda son zuciyarsu da burinsu, suka ji haushi da yadda babban taron jam’iyya ya gudana, tare da ganin cewa ba a kula da muradunsu na kashin kai ba a lokacin zaɓe."
"Sannan sai suka juya suka yi wa jam’iyyar adawa suka yi taƙaddama da ita. Mun sha fama da irin wannan matsala, rashin kunyar mutane suna raunana jam’iyya suna kuma yin watsi da ita.”
- Sule Lamido

Source: Twitter
Sule Lamido ya kuma sanar da cewa zai kaurace wa tarurrukan kwamitin amintattu (BOT) na jam’iyyar har sai an ɗauki matakin ladabtar da waɗanda yake zargin sun yi aiki don rusa PDP.
ADC: Sule Lamido ya hango kuskure a hadaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa akwai kuskure a cikin tafiyar hadakar 'yan adawa.
Sule Lamido ya bayyana cewa da yawa daga cikin 'yan siyasar hadakar suna sanya gaggawa wajen bayyana burinsu na yin takara.
Ya bukaci da su tsaya su fitar da tsari mai kyau kan yadda za su kawar da jam'iyyar APC daga kan madafun ikon Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
