Sule Lamido Ya Raba Gardama a PDP, Ya Hasko Wanda Zai Iya ba da Mamaki a Zaɓen 2027

Sule Lamido Ya Raba Gardama a PDP, Ya Hasko Wanda Zai Iya ba da Mamaki a Zaɓen 2027

  • Tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan na ta kara samun goyon baya daga kusoshin PDP duk da har yanzu bai ce komai ba
  • Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamdo ya shawarci PDP ta yi ƙoƙarin dawo da Jonathan domin shi ya fi dacewa da takarar shugaban ƙasa a 2027
  • Sule Lamido ya ce babu wani mamban PDP a yanzu da ya kama kafar tsohon shugaban ƙasar ta fannin kwarewa da iya shugabanci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce Goodluck Jonathan shi ne ɗan takara mafi ƙarfi da ya kamata PDP ta tsaida a zaɓen shugaban ƙasar 2027.

Sule Lamido ya shawarci jam'iyyar PDP da ta yi duk mai yiwuwa wajen shawo kan tsohon shugaban ƙasa, Jonathan domin ya dawo harkar siyasa gadan-gadan.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya samo mafita ga PDP kan mutanen da suka yi mata zagon kasa a 2023

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.
Sule Lamido ya bayyana cewa Jonathan ne ya fi dacewa PDP tsaida takarar shugaban ƙasa a 2027 Hoto: Sule Lamido
Asali: Facebook

Sule Lamido ya bayyana haka a hirar da aka yi da shi kan harkokin siyasar PDP a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin ɗin Channels ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule Lamido ya goyi bayan Jonathan a PDP

"Ina ganin yanzu ne lokacin da ya kamata PDP ta dawo da shi, shi ne zaɓi mafi kyau da za su tsaida takara, ba na ganin akwai wanda ya fi shi.
"Duk wanda jam'iyyar PDP ta ba tikitin takarar shugaban ƙasa, ƴan Najeriya za su mara masa baya."

- Sule Lamiɗo.

Sule ya ce Jonathan shi ne mafi dacewa a PDP a 2027 saboda ya taɓa shugabanci, ya fahimci yadda gwamnati take, kuma zai iya aiki da kowa cikin sauƙi.

Dalilan Sule Lamido na son a tsaida Jonathan

A cewar tsohon gwamnan, babu wani mamban PDP a yanzu daga Kudu da zai iya goga kafaɗa da Jonathan wajen kwarewa da sanin makamar aiki, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

2027: Ana shirin tarwatsa haɗakar Atiku da Peter Obi da kujerar minista mai tsoka

“PDP, APC, ADC, wannan zai zama abin sha’awa sosai. Muna maraba da shi ƙwarai, ƙwararre ne kuma ya cancanta matuƙa.
"Ni dai a wurina, ina maraba da shi. Har yanzu a PDP, da girmamawa ga dukkan mambobi, ban ga wani zaɓi mafi alheri fiye da Jonathan idan ya dawo PDP ba, ban ga wani mutum daban ba, gaskiya.
"Idan za mu bai wa Kudu takarar shugaban ƙasa, wane ne yanzu a PDP da zai iya kalubalantar Jonathan ta fuskar gogewa, hangen nesa, sauraron ra’ayoyin jama'a, wanda ya yarda da haɗin kai?"

- Sule Lamido.

Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.
Sule Lamido ya ce babu wanda zai iya ja da Jonathan a PDP Hoto: Dr. Goodluck Jonathan
Asali: Getty Images

Jonathan ya amince zai nemi takara a 2027?

Maganganun Sule Lamido sun zo ne a tsakiyar jita-jitar da ake ta yadawa kan yiwuwar Jonathan zai dawo PDP domin neman takarar shugaban ƙasa a 2027.

Jonathan, wanda ya koma gefe daga harkokin siyasa tun bayan kayen da ya sha a zaben shugaban ƙasa na 2015, bai fito ya bayyana cewa zai yi takara ba har kawo yanzu.

Kara karanta wannan

2027: An ji ra'ayin Jonathan kan fafatawa da Shugaba Tinubu

Wani dan PDP a karamar hukumar Danja ta Katsina, Abdullahi Kabir ya ahaida wa Legit Hausa cewa dawo da Jonathan shi ne mataki mafi kyau da PDP za ta dauka.

A cewarsa, har yan APC akwai wadanda sun fi gamsuwa da Jonathan fiye da Buhari, balle kuma Shugaba Bola Tinubu da ya lalata komai a kasar nan.

"Ni kaina ina tare da wannan shawarar ta dawo da Jonathan, na san tun lokacin Buhari na mulki yan Najeriya sun yi nadamar da ma tsohon shugaban ya dawo.
"Don haka muna rokon ahugabannin mu su taimaka au dawo mana da Shugaba Jonathan domin yana gogewa kuma ya san matsalar talakawa,'' in ji shi.

Ana zargin Jonathan na ƙoƙarin jawo Peter Obi

A wani labarin, mun kawo maku cewa Dumebi Kachikwu ya yi ikirarin cewa Jonathan ya yiwa Peter Obi tayin kujerar minista mai gwaɓi domin ya janye masa takara a 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu na tsaka mai wuya, PDP ta fara nuna wanda za ta tsayar takara a zaɓen 2027

Ya zargi cewa wasu ‘yan siyasa daga Arewa ne suka shigo da tsohon shugaban ƙasa Jonathan cikin takarar shugaban ƙasa domin rage ƙarfin Kudu.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Kachikwu, ya ce manyan Arewa ciki har da Atiku na amfani da damarsu wajen ɓata ƴan Kudu a wurin talakawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel