Kungiyoyin Arewa Sama da 1,000 Sun Tsaida Wanda Za Su Zaɓa tsakanin Tinubu da Atiku a 2027

Kungiyoyin Arewa Sama da 1,000 Sun Tsaida Wanda Za Su Zaɓa tsakanin Tinubu da Atiku a 2027

  • Gamayyar kungiyoyi sama da 1,000 na Arewa sun yi taro a Abuja kan wanda ya dace su marawa baya a zaɓen 2027
  • Shugaban gamayyar, Usman Abdullahi ya bayyana cewa tun da Najeriya ta samu ƴanci, ba a taɓa gwamnati mai aminci kamar ta Bola Tinubu ba
  • A cewarsa, gwamnatin APC ta kawo canjin da ya farfaɗo da Arewa, yana mai jaddada goyon baya ga tikitin Tinubu/Shettima

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ƙungiyoyin Arewa sama da 1,000 sun gana a babban birnin tarayya Abuja domin yanke wanda za su goyi baya tsakanin Atiku Abubakar, Bola Tinubu da sauran ƴan takara a 2027.

Ƙungiyoyin ƙarƙashin jagorancin gamayyar ƙungiyoyin ƴan Arewa daga jihohi 19 da Abuja (NPC) sun yi nazari kan ci gaban da Gwamnatin Shugaba Tinubu ta kawo.

Kara karanta wannan

Kimanin wata 1 da rasuwar Buhari, Adamu Maina ya auna mulkinsa da na Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyoyin Arewa sama da 1000 sun marawa Bola Tinubu da Kashim Shettima baya Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

The Nation ta rahoto cewa bayan kammala nazari, gamayyar ƙungiyoyin sun bayyana goyon baya ga Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima domin su yi tazarce a 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyin Arewa sun yabi gwamnatin Tinubu

Shugaban NPC na ƙasa, Usman Abdullahi, ya ce tun da Najeriya ta samu ƴanci shekaru 65 da suka gabata, ba a taɓa samun gwamnati irin ta Bola Tinubu ba.

Ya ayyana gwamnatin Tinubu-Shettima a matsayin “jagoranci mafi aminci” da aka samu a tarihin Najeriya, rahoton This Day.

Usman ya yabawa gwamnatin Tinubu bisa abin da ya kira, “farkon ci gaban siyasa da zamantakewa” wanda ya inganta Arewacin Najeriya.

Shugaban NPC ya jaddada irin canjin da gwamnatin ta kawo wajen magance matsalolin da suka daɗe suna damun yankin Arewa, wanda suka haɗa da koma baya wajen gina ababen more rayuwa.

NPC ta ce Bola Tinubu ya farfaɗo da Arewa

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027

"An daɗe ana yaɗa bayanai waɗanda ko kaɗan ba su kama ƙafar asalin halin da ake ciki a yankin Arewa ba, tun daga Bauchi zuwa Zamfara, daga Taraba zuwa Sakkawato.
"Amma, cikin ƙasa da shekaru biyu, Tinubu da Shettima sun kawo haske, suna aiwatar da manufofi masu kyau waɗanda suka ɗaga ƙimar Arewa a matsayin ginshiƙi a ƙasar Najeriya.”
“A karon farko, ‘yan Arewa suna rike da manyan mukamai a bangaren tsaro, kasuwanci, harkar man fetur, da ilimi, sune a gaba wajen gina sabuwar Najeriya.”

- In ji Usman Abdullahi.

NPC ta yi kira ga gwamnoni, ‘yan majalisa, sarakuna, da matasa da su yada manufar “sabunta fatan farfaɗo da Arewa”, tare da goyon bayan sake zaɓen Tinubu-Shettima a 2027 domin tabbatar da cigaban Najeriya.

Jonathan ya shirya gwabzawa da Tinubu a 2027

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP na ƙoƙarin dawo da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan domin ya gwabza da Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.

Wani na kusa da tsohon shugaban ƙasar ya ce Jonathan a shirye yake ya sake neman kujerar shugabancin Najeriya a zaɓe mai zuwa.

Ya kara da cewa Jonathan ya yanke shawarar shiga takarar ne domin neman hanyoyin da za su rage fatara, wahala da kuncin rayuwa da suka addabi 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262