'Har Yanzu El Rufa'i Yana APC, Yana ba da Shawari,' Jamoh Ya Fito da Bayanai

'Har Yanzu El Rufa'i Yana APC, Yana ba da Shawari,' Jamoh Ya Fito da Bayanai

  • Tsohon shugaban NIMASA, Bashir Jamoh, ya ce har yanzu tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai bai bar jam’iyyar APC ba
  • Bashir Jamoh ya ce duk da dangantakarsa da SDP da ADC, har yanzu suna shawara da Nasir El-Rufai a lokuta daban daban
  • Rahotanni sun bayyana cewa Bashir Jamoh ya bayyana El-Rufai a matsayin babban jagora kuma jigo siyasa a jihar Kaduna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Tsohon shugaban hukumar NIMASA, Bashir Jamoh, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, yana cikin jam’iyyar APC.

A cewar Jamoh, duk da cewa El-Rufai ya bayyana goyon bayansa ga jam’iyyun SDP da ADC, ba a taba samun wata sanarwa ta ficewar sa daga APC ba.

Tsohon gwamnan Kaduna da aka ce yana APC
Tsohon gwamnan Kaduna da aka ce yana APC. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya gudana a Kaduna ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Har yanzu El-Rufai na APC” – Jamoh

A yayin taron, Jamoh ya ce har yanzu El-Rufa'i yana taka rawa wajen bayar da shawarwari da hangen nesa ga tafiyar jam’iyyar.

Jamoh ya ce:

“A ra’ayina na, Malam Nasir El-Rufai har yanzu yana tare da mu. Eh, ya ambaci SDP, ya ambaci ADC, amma har yanzu ba mu kai matakin bankwana da shi ba. Har yanzu muna shawara da shi.”

The Guardian ta wa wallafa cewa ya cigaba da cewa:

“Muna neman shawararsa, iliminsa da kwarewarsa. A bar siyasa a gefe, wannan magana ce ta hidimar jama’a. Idan har ba zai ba da shawara ba idan an nema, to Allah zai tambaye shi.”

Jamoh: Ba za a yi watsi da El-Rufai ba

Jamoh ya kwatanta El-Rufai da wata cibiyar siyasar da ba za a iya cireta daga tarihi ba, yana mai cewa APC a Kaduna tana tare da shi.

Kara karanta wannan

APC ta gaza hakuri kan Atiku da El Rufa'i, ta fadi 'hadarin' da za su kawo a 2027

“Ba za ka iya korar ɗanka wanda ya girma da kai tsawon shekara takwas ba.
"Ya kasance minista a PDP, ya shiga CPC da ta hade da APC, kuma ya mulki wannan jiha tsawon shekara takwas. Shi ɓangare ne na tarihin siyasar mu,”

- In ji shi.

Dangantaka da ADC da tasirin El-Rufai

Game da rawar da El-Rufai ke takawa a jam’iyyar ADC, Jamoh ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da wani amfani a siyasar Kaduna.

“Har yanzu ba mu san waye ke cikin ADC a Kaduna ba. Eh, muna jin cewa shi ne shugaban yankin Arewa maso Yamma na ADC, amma a nan Kaduna ba su da tasiri,”

- In ji Jamoh.

El-Rufa'i tare da manyan 'yan adawa a Najeriya
El-Rufa'i tare da manyan 'yan adawa a Najeriya. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

El-Rufa'i ya yi magana kan 2027

A wani rahoton, kun ji cewa wani mai amfani da kafar sadarwa ya fusata tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i game da siyasar Najeriya.

Nasir El-Rufa'i ya yi martani da cewa sai bayan zaben 2027 za a gane matsayinsa a siyasa yayin da aka ce ba shi da katabus a yanzu.

Legit ta tattaro wasu daga cikin martanin da 'yan Najeriya suka yi game da maganar da tsohon gwamnan ya yi a a kan siyasar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng