'Ban Yi Nadama ba': Ministan Buhari Ya Faɗi dalilin Cire Shi daga Kujerar Gwamna
- Tsohon gwamnan Anambra, Chris Ngige, ya bayyana dalilin cire shi daga mukaminsa na gwamnan Anambra
- Sanata Ngige ya ce an cire shi ne saboda ƙin naɗa Chris Uba a matsayin mataimakinsa kamar yadda aka bukata
- Tsohon ministan kwadagon ya ce ya fi son rasa kujerarsa fiye da bai wa Uba mataimaki, saboda zai iya cutar da shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Sanata Chris Ngige, ya yi bayani kan dalilin cire shi a matsayin gwamna.
Ngige ya bayyana cewa cire shi daga kujerarsa a shekarar 2006 ya samo asali ne daga ƙin amincewarsa da bukatar naɗa Chris Uba a matsayin mataimaki.

Source: Facebook
Ngige ya magantu kan rasa kujerar gwamna
Sanata Ngige wanda ya rike ministan kwadago a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ya ce har yanzu yana cikin jam’iyyar APC, cewar Vanguard.
Ngige ya ce bai yi nadamar cire shi daga kujerar gwamna ba, yana mai cewa ya san waɗanda suka yi waje da shi.
Ngige ya ambaci wata ganawa da marigayi Sanata Ibrahim Mantu ya kawo masa sakon bukatar daga wasu manya na cewa ya naɗa Chris Uba ya zama mataimakin gwamna.
Ya ce:
“Da na naɗa shi, zai samu kariya ta doka, ya shigo ofishina, ya harbe ni, ba zai fuskanci hukunci ba.
“Mutanen Anambra za su tayar da hankali, su ƙi amincewa da hakan saboda sun san irin barnar da waɗanda suka goya Uba suka yi.”
Ngige ya ce sun ƙone ofishin majalisa, gidan gwamnati, gidan rediyon ABS da ofisoshin ilimi, kuma suka bayyana cewa ba za a bar shi ya dawo ba.
“Na ce, ku ɗauki kujerar. Ba matsala. Allah ne ke da iko. Idan wannan ce ƙaddara, zan rungume ta da zuciya ɗaya.”
- Cewar Ngige

Source: Facebook
Ngige ya kare kansa kan daukar yan daba
Sanata Ngige ya ce wani ya taɓa zuwa yana kuka saboda cire shi, sai ya ce masa zai iya kawo masa igiya idan yana so ya rataye kanka.
Ya kara da cewa bai nemi zuwa kotu ba saboda yana so a guje wa zubar da jini da sake tayar da rikici a jihar Anambra.
Ngige ya ce:
“Ba a haife ni gwamna ba. An haife ni a matsayin Nwabueze Ngige, ɗan wani kafinta wanda yake ma’aikaci a PWD.”
A cewarsa, yana hutu ne kawai daga APC, har yanzu yana cikin jam’iyyar duk da bai fito siyasa sosai ba yanzu, cewar Daily Post.
Ngige ya kuma bayyana dalilin ɗaukar wasu daga cikin ‘yan daba lokacin yana gwamna don yaƙi da laifi da rashin tsaro a jihar.
Ya ce amfanin kuɗin tsaro shine tabbatar da tsaron al’umma. Amma wasu gwamnoni suna ɗaukar shi a matsayin kuɗinsu.
Sanata Ngige ya gurfana a gaban ICPC
Mun ba ku labarin cewa tsohon minista, Chris Ngige ya gurfana a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.
ICPC ta titsiye Ngige kan zargin ya taka rawa a badakalar kwangiloli da kuma ta daukar ayyuka a lokacin ya ke kan kujerar minista.
Tsohon ministan ya kasance a gaban jami’an ICPC na tsawon sa’o’i biyar yana amsa tambayoyi kan kwangilolin da aka ba wata hukuma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


