Anambra: Jam’iyyar APC ta kai karar Chris Ngige wajen Shugaban kasa

Anambra: Jam’iyyar APC ta kai karar Chris Ngige wajen Shugaban kasa

- APC ta ce ‘Yanuwan Ministan kwadago rututu su ka samu mukamai a Gwamnatin Buhari

- Daga cikin na-kusa da Chris Ngige da su ka samu kujera a Gwamnati, har da Mai dakinsa

Wasu shugabannin jam’iyyar APC na reshen jihar Anambra, sun aikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika, su na masu gabatar da korafi.

‘Ya ‘yan jam’iyyar sun bayyanawa shugaban kasar cewa babu abin da APC ta tsinana tun da Dr. Chris Ngige ya zama Ministan tarayya daga jihar Anambra.

Jaridar Vanguard ta ce wadanda su ka sa hannu a wanna takarda su ne; Jideofor Ejimofor, Emeka Kammelu, Gody Offor, Henry Obiokpala, da Ugochukwu Egbobe.

Ragowar ‘ya ‘yan jam’iyyar da ke kuka da Ngige su ne: Joseph Molokwu, da Paul Chuks Umenduka.

KU KARANTA: An roki Gwamnatin Buhari ta dawo da aikin yasan Kogin Benuwai

A wasikar, ‘yan jam’iyyar sun godewa shugaban kasar na sake zaben Chris Ngige a matsayin Ministan, tare da kuma ba wasu 'yanu‘ansa da iyalinsa mukamai.

‘Ya ‘yan jam’iyyar sun mika godiyarsu na nada mai dakin Ministan, Dr. Evelyn Ngige a matsayin sakatariyar din-din-din a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Sannan yayan Ministan kwadagon, Emeka Ngige shi ne shugaban majalisar makarantun shari’a.

Wasikar ‘ya ‘yan jam’iyya ta tabbatar da cewa ‘yanuwar Ministan, Bene Nwachukwu da ‘danuwansa, Uzoma Igbonwa su na cikin shugabannin hukumar NACA.

KU KARANTA: Gwamna Sanwo-Olu ya bada labarin sana’ar da ya yi a lokacin baya

Anambra: Jam’iyyar APC ta kai karar Chris Ngige wajen Shugaban kasa
Chris Ngige Hoto: BBC
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar ta bayyana, ‘yan APC sun kuma godewa shugaba Muhammadu Buhari har ila yau, na ba baffan Ngige, Emma CJ Nwosu, kujera a gwamnatin tarayya.

Sai dai kuma sun ce: “Tun ranar 31 ga watan Yuli, 2013, da aka yi wa APC rajista da INEC, Chris Ngige ya zama shugaban jam’iyya a Anambra ba mu taba cin zabe ba.”

Takardar ta ce APC ba ta da tarihin nasara ko da a zaben kansila, karamar hukuma ko kuma majalisar dokoki, ko kuma majalisar tarayya zuwa kujerar gwamna.

A baya kun ji cewa Jigon APC a Kano, Abdulrahman Kawu Sumaila ya dura kan Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya ce 'dan siyasar bai da ilmin tarihin kafuwar APC.

Hon. Kawu Sumaila ya ce Gwamnan Imo bai da hurumin da zai yi magana a madadin Jam’iyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel