Sabon Shugaban APC da Gwamnoni Sun Gana da Sheikh Jingir, Malaman Izala da Darika
- Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar aiki ta farko a Jos tun bayan hawansa kan mulki
- Ya gana da Sheikh Sani Yahaya Jingir da Majalisar Malamai wanda ke kunshe da kungiyoyin Izala, Darika da JNI
- Sheikh Jingir ya bukaci shugabannin siyasa da su hada kai don magance matsalolin tsaro da inganta ilimi a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato – Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai wata ziyara ta musamman a garin Jos na jihar Filato, inda ya gana da manyan malamai da shugabanni.
Ziyarar, wadda ita ce ta farko da ya kai tun bayan hawansa kan kujerar shugabanci, ta samu tarba mai ban sha’awa daga magoya bayan jam’iyyar da jama’a.

Source: Facebook
Jam'iyyar APC ta wallafa a shafinta na X cewa Farfesa Nentawe Yilwatda ya gana da malaman addinin Musulunci da na Kirista yayin ziyarar.

Kara karanta wannan
APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin wadanda suka raka shi har zuwa Jos akwai gwamnonin jihohi, sanatoci da mambobin majalisar tarayya daga bangarori daban-daban na kasar nan.
Shugaban APC ya gana da malamai a Jos
Shugaban APC ya halarci taro tare da Majalisar Malamai ta Jos karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir.
Majalisar ta kunshi wakilai daga kungiyoyin Izala, Darika da kuma Jama’atu Nasril Islam (JNI), tare da wakilan sarakuna, ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma.
Shafin Jibwis Gombe ya wallafa a Facebook cewa Majalisar Malaman ta samo asali ne daga hadin kan jama’ar Musulmi a Jos, da nufin samar da jagoranci mai cike da hadin kai.
Jawabin Sheikh Jingir a taro da 'yan APC
Sheikh Jingir ya bukaci shugabannin siyasa da su hada karfi da karfe don shawo kan matsalolin tsaro a jihohinsu.
A bidiyon da Ibrahim Maina ya wallafa a Facebook, Malamin ya jaddada cewa ilimi mai inganci ne mafita, ba kawai mallakar takardun shaidar karatu ba.

Kara karanta wannan
APC ta gaza hakuri kan Atiku da El Rufa'i, ta fadi 'hadarin' da za su kawo a 2027
Ya kuma bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, da su ci gaba da aiki tare domin tabbatar da nasarar gwamnatin su da jin dadin al’umma.
Malamin ya jaddada matsayarsa kan goyon bayan gwamnatin Muslim Muslim da shugaba Bola Tinubu ke jagoranta.
Gwamnonin da suka raka shugaban APC Jos
Tare da Farfesa Nentawe sun kasance gwamna Usman Ododo na jihar Kogi, gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto da gwamnan jihar Imo.
Punch ta wallafa cewa bayan taron da Majalisar Malamai, shugaban APC ya gana da sarakunan gargajiya da sauran shugabannin addini, kafin ya koma Abuja.
Kakakin jam’iyyar APC na jihar Filato, Shittu Bamaiyi, ya ce jama’a da dama sun yi tururuwa tun karfe 8:00 na safe domin tarbar shugaban jam’iyyar a filin jirgin saman Yakubu Gowon.
APC ta soki El-Rufa'i da 'yan ADC
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta caccaki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i.
Kakakin APC, Felix Morka ya bayyana cewa kokarin Nasir El-Rufa'i na kalubalantar Bola Tinubu a 2027 ba zai yi nasara ba.
Morka ya kara da cewa ya fahimci akwai shirin tsayar da Atiku Abubakar takara a ADC, inda ya ce hakan ta saba tsarin karba karba tsakanin Kudu da Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng