Sule Lamido Ya Gano Babbar Matsalar 'Yan Hadaka, Ya Ba Su Shawara kan 2027

Sule Lamido Ya Gano Babbar Matsalar 'Yan Hadaka, Ya Ba Su Shawara kan 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ba da shawara ga jagororin da ke cikin hadaka karkashin jam'iyyar ADC
  • Sule Lamido ya nuna cewa jam'iyyar ADC tana cike da mutane masu gaggawar nuna aniyarsu ta tsayawa takara
  • Babban jagoran na adawa ya bukaci da su samo tsarin da za su yi amfani da shi wajen kifar da gwamnatin APC mai mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan hadakar 'yan adawa da ke karkashin jam'iyyar ADC.

Sule Lamido ya bayyana hadakar a matsayin jam’iyyar da ke cike da mutane masu gaggawa.

Sule Lamido ya yi magana kan ADC
Sule Lamido ya ba 'yan ADC shawara Hoto: @MSLAMIDO, @atiku
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Prime Time na tashar Arise tv a ranar Talata, 5 ga watan Agustan 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule Lamido ya yi magana kan jam'iyyar ADC

Kara karanta wannan

Haɗaka: Babbar matsala ta shiga ADC, ɗan majalisar tarayya ya ƙalubalance ta a kotu

Sule Lamido wanda ya halarci kaddamar da jam’iyyar ADC a watan Yuli, ya ce har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, yana mai cewa ba zai bar babbar jam’iyya ya koma ƙaramar jam’iyya ba.

Duk da haka, ya ba da shawara ga masu harin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ADC da su rage sauri kuma su yi taka-tsantsan a yadda suke tafiyar da shirin takarar su a zaben 2027.

Sule Lamido ya bayyana haka ne a daidai lokacin da ake ta tattaunawa a fagen siyasa dangane da alkawarin da Peter Obi ya yi na yin shekara hudu kawai idan aka ba shi damar shugabantar Najeriya.

Idan ba a manta ba dai kasa da awa 24 bayan kaddamar da jam’iyyar ADC, tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Kodayake tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, bai fito fili ya bayyana aniyarsa ba, ana rade-radin cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Wace shawara Sule Lamido ya ba 'yan hadaka?

Yayin da tattaunawa game da ADC ke kara karkata zuwa batun burin wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar, Sule Lamido ya ba da shawara ga masu burin tsayawa takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: El Rufai ya debo ruwan dafa kansa, APC ta yiasa martani mai zafi

Sule Lamido ya shawarci masu neman takarar da su rage gaggawa kuma su maida hankali wajen kawo ingantaccen tsari da zai ba su damar kayar da jam’iyyar APC mai mulki a 2027.

Sule Lamido ya ba 'yan hadaka shawara
Sule Lamido ya yi maganganu kan hadaka Hoto: Sule Lamido
Source: Twitter
"Ya kamata su natsu, su ci gaba da kulla alaka da jama'a a hankali, ta yadda idan sun fito gaba daya, za su yi karfi sosai."
"Ina ganin suna yin gaggawa sosai, akwai masu garaje da yawa a ciki. Ya kamata su rage gudu su duba al’amura da kyau, domin su samu damar cire wannan cuta mai suna APC."

- Sule Lamido

Sule Lamido ya jefi Tinubu da zargi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya nuna yatsa ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Sule Lamido ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na kokarin murkushe 'yan adawa ta hanyar yi musu cinne.

Ya bayyana cewa ana cinnawa 'yan adawa hukumomin yaki da ci hanci domin a yi musu barazana su koma jam'iyyar APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng