Haɗaka: Babbar Matsala Ta Shiga ADC, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Ƙalubalance Ta a Kotu
- Dan majalisa Leke Abejide ya soki dakatarwarsa daga jam’iyyar ADC, ya ce wasu "baƙi" suna kokarin kwace jam’iyyar da ya gina
- Hon. Abejide ya ce an dade da korar shugaban ADC na Kogi, Kingsley Ogga, tun 2022, don haka ba shi da ikon dakatar da kowa
- Ya bayyana cewa babu wata sahihiyar hadaka da wani ɓangare, ya ce hadakar ta mutu tun kafin a fara
- Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Lokoja, Kogi - Dan majalisar wakilai na ADC tilo, Leke Abejide, ya yi magana bayan jam'iyyar ta dakatar da shi.
Hon. Abejide ya gagara yin shiru kan dakatarwarsa daga jam’iyyar, yana mai watsi da kowane irin hadaka.

Source: Facebook
Dan majalisa ya kalubalanci ADC da hadakarta
Hon. Abejide ya bayyana cewa ba zai yarda wasu mutane baki su kwace jam’iyyar da ya sha wahala wajen kafawa ba, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abejide, wanda ke wakiltar mazabar Yagba a Majalisar Wakilai, ya bayyana haka ne yayin martani kan hadakar jam’iyyar ADC da kuma dakatarwar da Kwamitin Kogi ya yi masa.
Ya kalubalanci sahihancin dakatarwar, yana cewa shugabancin Kingsley Ogga ba ya kan doka, tunda an kore shi daga jam’iyyar tun 2022.
Ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda ake tafiyar da jam’iyyar, yana cewa babu gaskiya da bin kundin tsarin mulki.
Abejide ya ce lamarin ya kai kotu, kuma zai nuna musu cewa ba wai bai san abin da yake yi ba ne, cewar The Guardian.
Ya kara da cewa ya zama abin mamaki yadda shi kaɗai dan majalisa daga jam’iyyar, wasu daga waje za su zo su kwace iko da jam’iyyar.
Dan majalisar ya ce yana ƙin kowace irin hadaka, yana mai cewa hakan kuskure ne da ba za a iya gyarawa ba.
“Babu hadaka saboda ba za ta yiwu ba. Ina da hurumin kalubalantar dukan matakan da suka dauka a kotu.
“Hadakar me? Wannan hadaka ta mutu tun kafin ta fara. Mu je zabe mu ga wanda zai yi nasara. Kuskure an riga an tafka.
- In ji Abejide

Source: Twitter
Shawarar da Abejide ya ba ADC a Najeriya
Ya shawarci jagorancin Sanata David Mark da su canja salo, su nemi sabon tsari domin ADC ba za ta shiga cikin wannan tafiya ba.
Hon. Abejide ya bayyana cewa kundin tsarin jam’iyyar ya tanadi taron NEC kafin a samu sauyin shugabanci.
Jagoran ADC ya ce ya maka sabbin shugabannin da ba a san su ba a kotu, yana masu cewa ba su da matsayin doka a jam’iyyar.
Abejide ya bukaci a bi doka da tsarin kundin jam’iyyar domin a samu shugabanci na gaskiya da bin ƙa’ida.
Hon. Abejide ya yi wa ADC gori
Kun ji cewa jam'iyyar ADC na ci gaba da fuskantar matsala tun bayan haɗewa da jagororin adawar Najeriya.
Hon. Leke Abejide ya bayyana cewa babu inda wannan haɗaka za ta je domin ba za su iya ja da APC ba.
Ya yi barazanar cewa zai iya barin ADC da ya gina zuwa APC a duk lokacin da ya ga dama domin yana da ƴancin yin hakan.
Asali: Legit.ng

