Ibrahim Namadi da Kwamishinonin Kano 2 da Suka Ajiye Aiki a Gwamnatin Abba Yusuf

Ibrahim Namadi da Kwamishinonin Kano 2 da Suka Ajiye Aiki a Gwamnatin Abba Yusuf

  • A 2025, akalla kwamishinoni uku sun ajiye aiki a jihar Kano, ciki har da Muhammad Diggol, kwamishinan kula da ayyukan gwamnati
  • Injiniya Muhammad Diggol ya yi murabus ne a Janairun 2025 jim kadan bayan da aka dakatar da shi daga jam'iyyar NNPP a jihar Kano
  • Legit Hausa ta jero sunayen kwamishinonin Kano uku da suka ajiye aiki a 2025 tare da yin bayani kan martanin gwamnatin Abba Yusuf

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - 'Yan majalisar zartarwar jihar Kano da dama sun yi murabus a karkashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf a shekarar 2025.

Na baya bayan nan shi ne Alhaji Ibrahim Ali Namadi, kwamishinan zirga-zirga da ya yi murabus a ranar 6 ga watan Agusta, 2025.

Kwamishinonin Kano 3 sun yi murabus a shekarar 2025 saboda wasu dalilai daban daban
Gwamna Abba Yusuf ya amince da murabus din kwamishinan sufuri, Ibrahim Namadi. Hoto: @HonAbdullahiM12
Source: Twitter

Nadin kwamishinoni da murabus din wasu

Kafin murabus din Alhaji Ibrahim Namadi, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu kwamishinoni sun yi murabus daga gwamnatin Abba Yusuf saboda dalilai daban daban.

Kara karanta wannan

Belin dilan ƙwaya: Kwamishinan Abba a jihar Kano ya yi murabus

A farkon mulkinsa a 2023, Gwamna Abba Yusuf ya mika sunayen kwamishinoni ga majalisar dokokin Kano, kuma a 26 ga Yunin 2023 ya rantsar da sababbin kwamishinonin 17.

A watan Disambar 2024, gwamnan ya sake mika sunayen sababbin kwamishinoni bakwai ga majalisar jihar, sannan ya rantsar da su a Janairun 2025.

A wannan rahoton, mun jero kwamishinonin jihar Kano da suka yi murabus a shekarar 2025 da bayani kan dalilan da ya sa suka ajiye aiki.

Kwamishinonin Kano 3 da suka ajiye aiki

1. Injiniya Muhammad Diggol

A ranar 5 ga watan Janairun 2025, mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanar da cewa Muhammad Diggol, kwamishinan kula da ayyukan gwamnati ya yi murabus.

Mun ruwaito cewa Muhammad Diggol ya ajiye aiki ne ana dab da rantsar da sababbin kwamishinonin da majalisar dokokin Kano ta amince da su.

"Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din Injiniya Muhammad Diggol, kwamishinan kula da ayyukan gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike kan zargin kwamishina da belin dilan ƙwaya

"A farkon gwamnatin Abba Yusuf a 2023 aka nada Injiniya Muhammad Diggol matsayin kwamishinan zirga-zirga.
"Amma daga bisani aka sauya masa mukami zuwa kwamishinan kula da ayyukan gwamnati, inda ya yi aiki har zuwa murabus dinsa a yau."

- Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa duk da ba a bayyana dalilin yin murabus ɗin Injiniya Diggol ba, lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan sauyin da aka yi wa majalisar zartarwa ta jihar.

Sannan kafin wannan lokaci, NNPP ta dakatar da Diggol tare da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. Abdullahi Baffa Bichi bisa zargin rashin biyayya ga shugabancin jam’iyyar.

2. Manjo Janar Muhammad Idris (mai ritaya)

A ranar Laraba, 26 ga Maris din 2025 muka ruwaito cewa Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya) ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kano.

An naɗa Muhammad Idris a matsayin kwamishinan sabuwar ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida da Gwamna Abba ya kirkira a watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya yi garambawul a gwamnatinsa, ya sauya mukaman kwamishinoni

Mai Magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar, yana mai cewa:

"Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din kwamishinan sabuwar ma'aikatar tsaron cikin gida da harkoki na musamman, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya)."

Duk da cewa bai yi wani dogon zango a mukamin nasa ba, amma gwamnatin Kano ta ce Muhammad Idris ya kafa harsashi mai karfi na gudanarwar ma'aikatar.

Kwamishinan sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi ya yi murabus bayan karbar belin dilar kwaya
Kwamishinan sufurin Kano da ya yi murabus, Ibrahim Ali Namadi. Hoto: @HonIsahUmar
Source: Twitter

3. Alhaji Ibrahim Ali Namadi

A safiyar Alhamis, 6 ga watan Agusta, 2025 aka tashi da labarin murabus din kwamishinan sufuri na Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi.

Mun ruwaito cewa Namadi ya ajiye aiki sa’o’i kadan bayan Gwamna Abba ya karɓi rahoton kwamitin bincike kan zargin shi da karbar belin dilan ƙwaya, Sulaiman Aminu Danwawu.

Sanusi Dawakin Tofa ya fitar da sanarwa a safiyar Alhamis cewa:

"Kwamishinan ya yanke shawarar yin murabus din ne domin kwantar da hankulan jama'a la'akari da girman lamarin."

Yayin da Alhaji Ibrahim Namadi ya dage cewa bai aikata wani laifi ba, amma ya ce ba zai kuma kawar da kai daga yadda jama'a suke kallon lamarin ba, don haka ya ajiye aiki don kare martabar abin da aka dade ana ginawa.

Kara karanta wannan

Dilan ƙwaya: Bayanai sun bulloƙo kan kwamishinan Kano, ana zargin ya karbi $30,000

Ya kuma yi godiya ga Gwamna Abba Yusuf bisa damar da ya ba shi ta yiwa al'ummar jihar hidima, tare da ci gaba da ba da goyon baya ga gwamnatinsa.

Abba ya rantsar da kwamishinoni a Kano

Tun da fari, mun ruwaito cewa, sababbin kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da aka naɗa a jihar Kano sun karbi rantsuwar aiki.

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sababbin masu muƙaman ne a gidan gwamnati a ranar Litinin, 6 ga watan Janairun 2025.

Abba Kabir Yusuf ya buƙaci masu muƙaman da masu maida hankali wajen sauke nauyin da aka ɗora musu domin kawo ci gaba mai dorewa a jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com