'Tinubu Zai Kori Wike,' Sule Lamido Ya Fito da Bayanai kan Ministan Abuja

'Tinubu Zai Kori Wike,' Sule Lamido Ya Fito da Bayanai kan Ministan Abuja

  • Tsohon gwamnan Jigawa ya ce ba Nyesom Wike mukami wani salo ne na siyasa da shugaba Bola Tinubu ya yi
  • Sule Lamido ya ce idan Tinubu ya samu gindin zama a jihohin yankin, zai kori Wike domin ya gama amfani da shi
  • 'Dan siyasar ya shawarci gungun jam'iyyun adawa da su natsu su fahimci al'amura kafin su kalubalanci APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi magana kan nadin Nyesom Wike a matsayin ministan Abuja da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Sule Lamido ya ce hakan wani yunkuri ne na tabbatar da tasirinsa a yankin Kudu maso Kudu na kasar.

Sule Lamido ya ce a gaba Tinubu zai kori Wike
Sule Lamido ya ce a gaba Tinubu zai kori Wike. Hoto: Bayo Onanuga|Nyesom Wike|Sule Lamido
Source: Facebook

Lamido ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa na tashar Arise TV a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Minista ya kwadaitawa Ibo mulkin Najeriya, ya ce taimakon Tinubu zai kai su Aso Rock

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamido ya yi zargin cewa wannan matsayi da aka ba Wike ba zai dawwama ba, domin Tinubu zai yi watsi da shi da zarar ya cimma burinsa na siyasa a yankin.

Ya ce tuni Shugaban kasa ya samu dama a jihohin Akwa Ibom, Edo da Delta, yayin da Wike ke da karfi a jihar Rivers.

'Tinubu zai kori Wike' — Sule Lamido

Sule Lamido ya ce Tinubu yana yin amfani da dabarun siyasa domin samun rinjaye a Kudu maso Kudu, yana mai cewa an bai wa Wike mukami ne domin amfani da karfinsa a yankin.

A cewar shi, daga lokacin da Tinubu ya samu rinjaye a duka yankin, babu abin da zai hana a raba Wike da mukaminsa.

The Cable ta wallafa cewa ya ce:

"Yanzu haka, ta hanyar amfani da dabaru da matsin lamba, Tinubu ya samu rinjaye a Akwa Ibom, Edo da Delta. Wike kuwa tuni ya rike Rivers,"

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027

"Da zarar ya shawo kan Kudu maso Kudu, Wike ba zai kara amfani ba, kuma zai yi watsi da shi."
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido. Hoto: Sule Lamido
Source: Twitter

Shawarar Sule Lamido ga jam'iyyar ADC

A bangare guda, Lamido ya yi tsokaci kan halin da jam’iyyun adawa ke ciki, musamman gungun da ke karkashin ADC.

Ya ce akwai gaggawa da rashin natsuwa a cikin tafiyar ADC, yana mai bada shawarar su zauna su tantance al’amura cikin hankali da hangen nesa.

"Ya kamata su rage gudu, su yi tunani mai zurfi kan matsalolin da ke gaban su,"

- In ji shi.

Ya kara da cewa:

"Su ci gaba da hada kai da mutane a cikin sirri, su yi turakun hadin kai kafin su fito da karfi gaba daya."

Sule ya kammala da cewa idan 'yan adawa suka yi taka tsantsan da dabaru masu karfi, za su iya karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC da ya kira "cutar da ke damun Najeriya."

Sule Lamido zai yi wa ADC aiki

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce har yanzu yana jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Yaki zai kare: Bello Turji ya ajiye makamai bayan haduwa da malaman Musulunci

Sai dai duk da haka, Sule Lamido ya bayyana cewa zai cigaba da yi wa jam'iyyar ADC aiki domin samun nasara a 2027.

Tsohon gwamnan ya yi bayani ne yayin da 'yan adawa ke kokarin kafa dandali mai karfi a ADC domin tunkarar APC a zabe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng