Jigon a APC Ya Gano Dalili 1 da Zai Hana 'Yan Arewa Zabar Peter Obi a 2027

Jigon a APC Ya Gano Dalili 1 da Zai Hana 'Yan Arewa Zabar Peter Obi a 2027

  • Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Alwan Hassan ya yi magana kan takarar Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2027
  • Alwan Hassan ya bayyana cewa Peter Obi ba zai samu kuri'un 'yan Arewa ba saboda sana'arsa ta shigo da barasa
  • Hakazalika 'dan siyasar ya yi watsi da hadakar 'yan adawa wadda ke son kifar da gwamnatin Bola Tinubu a 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Alwan Hassan, wani jigo daga Arewacin Najeriya a jam’iyyar APC mai mulki, ya bayyana cewa Arewa ba za ta kada wa Peter Obi ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.

Jigon na APC ya ce Arewa ba za ta zabi Peter Obi ba saboda yana da hannu wajen shigo da giya a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

APC ta yi wa Tinubu alkawari yayin da ta jaddada mubaya'a ga Ganduje a Kano

Jigon APC ya taso Peter Obi a gaba
Jigon APC ya ce Peter Obi ba zai samu kuri'un Arewa ba Hoto: @PeterObi
Asali: Facebook

Alwan Hassan ya yi wannan furuci ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Tv a ranar Talata, 5 ga watan Agustan 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me jigon na APC ya ce kan Peter Obi?

Ya bayyana cewa Peter Obi ba zai iya yin nasara kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

"Waye kuma kake ganin zai iya doke Asiwaju a 2027? Waye? Peter Obi wanda a shirinku ya ce yana son Arewa ta mara masa baya, amma a cikin wannan shirin yake murnar buɗe kamfanin giya a jihar Anambra kuma yana ɗaya daga cikin manyan masu shigo da giya kasar nan."
"Kuma kana son mu Arewa mu kada masa ƙuri’a? Mu zabi shugaban ƙasa da zai shigo mana da giya a Arewa?”

- Alwan Hassan

Jigon na APC ya yi tambaya kan hikimar tsayar da ɗan takara wanda harkokinsa na kasuwanci sun sabawa al’adu da addinin Musulunci na mafi yawan mutanen yankin Arewa.

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027

Peter Obi, wanda ya sanar da niyyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027 tare da alkawarin yin wa’adi ɗaya kacal, yana fuskantar suka daga jiga-jigan APC tun bayan wannan sanarwar tasa.

Alwan Hassan ya yi watsi da hadaka

A ci gaba da jawabin nasa, Alwan Hassan ya yi watsi da hadakar 'yan adawa ƙarƙashin jam’iyyar ADC, yana mai cewa ba ta da ƙarfi, kuma an kafa ta ne bisa son zuciya da burin kowane ɗan siyasa, ba don wani buri na bai ɗaya ba.

"ADC gamayyar wasu mutane ne da suka fusata, amma suna da dabarar siyasa. Kowane ɗayansu yana son zama shugaban ƙasa. Asiwaju ne zai ci gaba da zama shugaban ƙasa.”

- Alwan Hassan

Jigon APC ya yi kalamai kan Peter Obi
Jigo a APC ya ce Peter Obi ba zai ci zabe a Arewa ba Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Hadakar 'yan adawar dai ta haɗa da fitattun mutane irin su Peter Obi, Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai da sauransu, tun bayan kafuwarta ta ke bayyana kanta a matsayin madadin jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

An fadi yadda Tinubu ya kafa tubali mai karfi a Arewa don doke Atiku da Obi

Amma a cewar Alwan Hassan, ƙoƙarinsu ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Ya ce gwamnatin Tinubu za ta ƙarfafa matsayinta, kuma za ta sake lashe zaɓe a 2027.

Hadimin Peter Obi ya kare maigidansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin Peter Obi ya fito ya kare magidansa kan zargin yana shirin kifar da gwmanatin Shugaba Bola Tinubu.

Valentine Obienyem ya bayyana cewa babu komai a cikin zargin face tsagaben karya da rashin gaskiya.

Hakazalika ya bukaci hukumomi da su gudanar da bincike kan mutanen da suke yada zargin kitsa juyin mulkin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng