2027: Yadda aka Samu Shugabanni 2 ko Fiye a ADC da Wasu Jam'iyyun Adawa a Najeriya
Rikicin cikin gida ya dabaibaye manyan jam'iyyun adawa a Najeriya yayin da suke kokarin kafuwa domi tunkarar APC a zaben 2027.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam'iyyun adawa da suka hada da ADC, PDP, LP da NNPP na cigaba da fuskantar kalubalen da ya shafi rikicin cikin gida.
Rikicin ya kai ga haifar da sabani musamman a bangaren shugabanci ta inda aka samu shugabanni har biyu a wasu jam'iyyu.

Asali: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa tayi nazari kan yadda wasu jam'iyyu kamar ADC da sauransu suka samu wasu na ikirarin zama shugabanni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. An samu shugabanni 2 a jam'iyyar ADC
Jam’iyyar ADC na fuskantar rikicin cikin gida bayan karɓar tsofaffin ’yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi, domin samar da kafar adawa da za ta fuskanci APC a zaben 2027.

Kara karanta wannan
APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027
Wannan sauyi ya zo ne bayan rarrabuwar ƙuri’u a zaben 2023 da ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu nasara, lamarin da ya sa ’yan adawa ke neman haɗa kai.
Biyo bayan wannan sauyin, tsohon shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Ralph Nwosu, ya mika ragamar shugabanci ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark.

Asali: Facebook
Sai dai rahotanni sun nuna cewa ba kowa ne a ADC ke goyon bayan wannan sauyin ba, wasu shugabannin jihohi da mambobin jam’iyyar na asali sun nuna rashin amincewa.
Ɗan takarar gwamnan Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar ADC a zaben 2023, Nafiu Bala, ya fito fili yana sukar matakin.
A wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, Bala ya bayyana kansa a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar ADC.
2. Mutane 3 na ikirarin zama shugabannin LP
Jam’iyyar LP a Najeriya na fama da rikicin shugabanci, inda mutane biyu ke ikirarin zama shugabannin jam’iyyar na kasa; Julius Abure, Lamidi Apapa da Nenadi Usman.
Abure na ganin kan shi a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa, kuma yana jagorantar wani ɓangare da ke ganin shi ne sahihin shugaba, tare da goyon bayan wasu shugabannin jihohi.
Tsagin Abure na zargin Peter Obi da gwamnan jihar Abia, Alex Otti, da haddasa rikici a cikin jam’iyyar.

Asali: Facebook
Wani ɓangare na LP ya amince da Nenadi Usman a matsayin shugabar jam’iyyar ta ƙasa, inda hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da Kotun Koli suka tabbatar da jagorancinta a watan Afrilun 2025.
Nenadi Usman na samun cikakken goyon bayan Peter Obi da Gwamna Otti, waɗanda ke ganin jagorancinta a matsayin hanyar haɗa kan jam’iyyar domin babban zaɓe na 2027.
Shi kuma Lamidi Apapa ya dage cewa shi ne shugaban jam'iyyar, ko kwanan Premium Times ta rahoto cewa ya sake yin wannan ikirari, yana da dogara da hukuncin kotun koli.
3. Jam'iyyar NNPP ta rabu 2 a Najeriya
Jam’iyyar NNPP ta rabu gida biyu; ɓangaren da ke da biyayya ga Rabiu Kwankwaso ƙarƙashin Dr. Ajuji Ahmed, da kuma wani ɓangare da ke ƙarƙashin Boniface Aniebonam.
Aniebonam da Dr. Agbo Major sun bayyana cewa su ne sahihan shugabannin jam’iyyar, suna kalubalantar doka da tsarin mulkin NNPP da kuma Kwankwaso.

Asali: Facebook
A cewar su, jam’iyyar na bukatar sabon jagora da zai dawo da martabar ta da kuma tsaftace tsarin shugabanci.
Daily Trust ta wallafa cewa bangaren da ke da biyayya ga Rabiu Kwankwaso ya ce jam’iyyar na karkashin kulawarsu.
Dr. Ajuji Ahmed shi ne shugaban NNPP na kasa wanda Kwankwasiyya ta yi amanna da shi, kuma ta na ikirarin shi INEC ta sani.
4. An samu shugabanni 2 a SDP
Adamu Modibbo ya bayyana kansa a matsayin sabon mukaddashin shugaban jam’iyyar SDP yayin da Shehu Musa Gabam ke rike da shugabancin jam'iyyar.
Rahoton VON ya nuna cewa ’yan jam’iyyar SDP a jihohin Imo da Bauchi sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shehu Musa Gabam da suka ce shi ne sahihin shugaba.
Sun yi kira ga sauran shugabannin jam’iyyar a jihohi da ƙananan hukumomi da su bi sawun jagorancin Gabam.

Kara karanta wannan
ADC: El Rufai da manyan ƴan siyasar Kaduna da suka fice daga PDP, APC, suka shiga haɗaka

Asali: Facebook
APC ta zargi ADC da neman kawo rikici
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta zargi ADC da kokarin zama barazana ga zaman lafiya a Najeriya.
Kakakin APC, Felix Morka, ya zargi tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i da kokarin rusa tsarin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa.
Morka ya bayyana haka ne yayin da ya zargi ADC da kokarin tsayar da Atiku Abubakar takara a 2027 duk da cewa daga Arewa ya ke.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng