APC Ta Yi Watsi da Kalaman El Rufai, Ta Fadi Dalilin da Zai Sa Tinubu Yin Tazarce a 2027
- Jam'iyyar APC ta nuna kwarin gwiwa kan batun tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 da ake tunkara
- Sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, ya bayyana cewa 'yan Najeriya za su sake zaben Shugaba Tinubu a karo na biyu
- Felix Morka ya kuma yi watsi da kalaman tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai wanda ya soki kamun ludayin gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa tana da tabbacin cewa ‘yan Najeriya za su sake zabar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027,
Jam'iyyar APC ta bayyana wa’adi na farko na mulkin Shugaba Tinubu a matsayin daya daga cikin mafi fice a tarihin Najeriya.

Asali: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka, ya fitar a ranar Litinin a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta yi wa Nasir El-Rufai martani
Felix Morka ya kare nasarorin gwamnatin Tinubu a matsayin martani kan sukar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi kwanan nan.
Mai magana da yawun na APC ya yi watsi da kalaman da El-Rufai ya yi a Sokoto ranar 2 ga Agusta, inda ya soki gwamnatin Tinubu kan cewa ba ta da ƙwarewa, tana nuna son kai, kuma ba ta cancanci wa’adi na biyu ba.
Jam’iyyar APC ta ce El-Rufai da abokan tafiyarsa a ADC ba su da wani shiri kwatankwacin sauye-sauyen tattalin arzikin da Tinubu ke aiwatarwa, manufofin da su Atiku Abubakar da Peter Obi suka yi alkawarin aiwatarwa a zaben 2023.
"Idan har sun tsani wadannan sauye-sauyen kamar yadda suke ikirari, meyasa ba su fito fili suka ce za su dawo da tallafin mai da tsarin musayar kudi ba, tare da bayyana yadda za su samu kudin da za su biya gibin da hakan zai haifar ba?"

Kara karanta wannan
El Rufai ya hango babbar matsalar da za ta auku idan APC ta ci gaba da mulkin Najeriya
- Felix Morka
Ya jaddada cewa shirin gwamnatin Tinubu na (Renewed Hope Agenda) ya sake daidaita tsarin kasar nan don habaka ta zuwa kan turbar ci gaba.
Jam’iyyar ta bayyana ci gaba a fannoni kamar noma, ababen more rayuwa, samar da man fetur, ba dalibai bashi, da daidaiton tattalin arziki a matsayin shaida kan nasarorin da gwamnatin ta cimma zuwa yanzu.
Meyasa za a sake zaben Tinubu a 2027?
A cewar APC, wadannan sauye-sauye da nasarori ne za su sanya ‘yan Najeriya sake kada kuri’arsu ga Tinubu a zaben 2027.

Asali: Facebook
"Najeriya na cikin wani sabon zamani na jagoranci mai hangen nesa da sauyi karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu."
"Muna da tabbacin cewa ‘yan Najeriya za su ci gaba da marawa babbar jam’iyyarmu baya tare da sake damka amana ga Shugaba Tinubu a 2027."
"Domin ci gaba da yin abin da aka bayyana a matsayin mafi gagarumar nasara a wa’adi na farko da kowanne shugaban kasa ya taba samu a tarihin Najeriya."
- Felix Morka
Jam'iyyar APC ta ragargaji El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta caccaki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
APC ta shawarci El-Rufai kan ya daina gaggawa, ya jira sai lokaci ya yi kafin ya fara yakin neman zaben 2027.
Hakazalika ta bayyana cewa ya kamata tsohon gwamnan ya je ya nemi abin yi maimako maida hankali kan sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng