'Dalilin da Ya Sa Jam'iyyar PDP Ke Son ba Goodluck Jonathan Takara a Zaɓen 2027'
- Wasu jiga-jigan PDP sun fara shirin dawo da Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa a 2027, inda ya fara amince da bukatar
- Mataimakin sakataren yada labaran PDP ya ce Jonathan ya cancanci a sake nemansa saboda irin yadda ya jagoranci kasar a baya
- Ya ce mutane da dama suna kira da a dawo da Jonathan saboda yadda ya mika mulki cikin sauki a 2015, ba tare da rikici ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Majiyoyi sun tabbatar da shirin wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP a Najeriya game da kwace mulki a zaben 2027.
An tabbatar da cewa wasu manyan jam'iyyar ciki har da gwamnoni na duba yiwuwar dawo da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Asali: Facebook
An fara dakon Jonathan ya dawo a 2027
Tashar BBC Hausa ta tattauna da mataimakin sakataren yada labaran PDP, Ibrahim Abdullahi inda ya tabbatar da haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon na PDP ya ce Jonathan ya amince da bukatar duk da kafa wasu sharuda da ya yi game da takarar.
Ibrahim Abdullahi ya tuna irin mulkin Goodluck Jonathan a wancan lokaci kasancewarsa dan PDP ya ce ba laifi ba ne a sake nemo shi.
Ya ce:
"Abubuwan da wannan bawan Allah ya yi lokacin da yake rike da mulki, mu ka ga babu laifi tun da har yanzu yana PDP a sake nemo shi.
"Yan Najeriya sun fahimci abin da suke zarginsa a baya ba laifinsa ba ne har ma suna ba shi hakuri ya zo ya cece su.
"Mummunar fahimtar da suka yi masa a baya sun gane ba haka ba ne, sun gane yana da tausayi."

Asali: UGC
Yadda yan Najeriya ke yabon Jonathan
Ibrahim Abdullahi ya ce mutane da dama sun yabawa Jonathan kan abin da ya faru a lokacin zaben 2015 inda ya mika mulki cikin sauki.

Kara karanta wannan
'Sau 3 muna zama da Turji a wata 1': Shehin malami ya ja hankalin hukumomi kan sulhu
Ya ce wadannan na daga cikin abin da ya sa aka neman ya dawo ba wai ra'ayin yan jam'iyyar PDP ba ne kawai.
Ya kara da cewa:
"A lokacin da ya fadi zaben nan yana da ikon yin magudin zaben amma ya ga jinin dan Najeriya guda ya fi muradinsa, ya yi hakuri ya karbi faduwarsa har da taya murna.
"Wadannan abubuwan da ya yi ya sa yan Najeriya ke kira ba kawai mu yan jam'iyya ba, mu kuma daman yan Najeriya muke ma biyayya sai muka ga hakan ya kyautu.
"Ya fara sauraren bukatarsa da ake yi kuma ya ba da sharuda cewa za a hada shi takarar share fage da wasu ko kuma da gasken ake an fahimci ingancinsa na tsayawa takara?.
"Sannan shi ma zai tuntuba da kuma shawara da na kusa da shi kan bukatar da ake yi masa."
'Ana shirin dawo da Jonathan' - Bashir Ahmad

Kara karanta wannan
Bayan bidiyon Ummi Nuhu, Mai Dawayya ya yi tone tone, ya faɗi shura da ya yi a baya
Mun ba ku labarin cewa tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad ya ce akwai wani shiri da ake kullawa kan Goodluck Ebele Jonathan.
Bashir Ahmad ya bayyana cewa akwai masu son ganin an kawo tsohon shugaban kasa ya sake neman takara a zaben shekarar 2027.
Dan siyasar ya bayyana cewa ana son yin wannan shirin ne don samun kuri'un 'yan Arewa, yankin da ya fi ko ina yawan al'umma a kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng